’Yan bindiga sun kai wa tawagar Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, hari a Owerri, Jihar Imo, da safiyar ranar Talata.
An kai masa harin ne a kusa da Filin Jirgin Sama na Sam Mbakwe, amma Gwamna Otti ba cikin ayarin lokacin da aka kai harin.
- An Kusa Ceto Ɗaliban Neja Da Aka Sace – Ribadu
- Sin Ta Yi Kira Ga Japan Da Ta Gyara Kalaman Kuskure Tare Da Dakatar Da Kaucewa Gaskiya
Ya zuwa yanzu babu rahoton wanda ya rasa ransa ko wanda ya jikkata.
Lamarin ya faru ne tsakanin Umuowa zuwa mahaɗar Ihite, kafin a ƙarasa filin jirgin sama.
Har zuwa yanzu, ’yansandan Jihar Imo ba su fitar da wata sanarwa kan harin ba.
Sakataren Gwamna Otti kan Harkokin Yaɗa Labarai, Ukoha Njoku, ya bayyana lamarin a matsayin “abin baƙin ciki” kuma ya tabbatar wa jama’a cewa gwamnan yana cikin ƙoshin lafiya.
Haka kuma ya gode wa jami’an tsaro bisa saurin ɗaukar mataki wajen tsare yankin.
Har yanzu ba a san dalilin kai harin ba, kuma hukumomi suna gudanar da bincike.
Mazauna yankin da fasinjoji sun shiga firgici, amma babu wanda ya jikkata, sai dai an dakatar da zirga-zirga na ɗan lokaci a yankin.














