Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne a ranar Laraba, sun kaddamar da munanan hare-hare kan al’ummar Motokun da Agboro da ke karamar hukumar Patigi a jihar Kwara, inda suka kashe jami’in ɗansanda ɗaya da wata mata tare da yin awon gaba da mutane shida.
‘Yan ta’addan da suka mamaye al’ummar jihar Kwara ta Arewa da sanyin safiyar Laraba, sun kuma harbi mutum shida.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Kwara, Toun Ejire-Adeyemi, a wata sanarwa da ya fitar a yammacin Laraba, ya tabbatar da cewa, wata mata ta mutu sakamakon harbin bindiga da ta samu a yayin harin.
Ta kuma tabbatar da yin garkuwa da mutane shida a yankunan biyu, inda ta kara da cewa wasu shida sun samu raunuka a harbin bindiga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp