Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun kashe basaraken ƙauyen Luma Baale da wasu mazauna yankin da dama a ƙaramar hukumar Borgu ta Jihar Neja.
Rahotanni sun ce maharan sun kuma ƙona gidaje tare da ƙona gawar wasu daga cikin waɗanda suka kashe.
Wani mazaunin yankin, Mohammed Alhassan, ya ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 5 na safiyar ranar Asabar, lamarin da ya tilasta wa mutane da dama tserewa zuwa daji domin neman mafaka.
Ya ce wasu daga cikin mazauna yankin sun koma garin Luma, inda jami’an tsaro suke.
Alhassan ya zargi wasu matasan Fulani daga cikin al’ummar ƙauyen da haɗa kai da ’yan bindiga wajen kai harin.
Sabon harin ya ƙara tayar da hankali kan matsalar tsaro a masarautar Borgu, wadda ta sha fuskantar hare-haren ’yan bindiga da satar mutane da yawa.
A baya-bayan nan, an sace ɗalibai sama da 200 a wata makarantar Katolika da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara, yayin da aka kuma sace masu ibada daga wani masallaci a Dakera.
Rahotanni sun ce har yanzu ’yan bindiga na tsare da ɗaruruwan mutanen da suka sace a yankin.
Hare-haren da ake ci gaba da kaiwa sun ƙara jawo hankalin jama’a kan tabarbarewar tsaro a masarautar Borgu, wadda ke da alaƙa da sarautar gargajiya ta Jagaban Borgu da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke riƙe da ita.













