‘Yan bindiga sun sake kai hari a karamar hukumar Wase tare da kashe hakimin kauyen Nyalun, Salisu Idris.
An rawaito cewa an kuma kashe wasu mazauna garin biyu a yayin harin wanda ya faru a daren ranar Litinin.
- Fyade: An Yi Wa Wani Mutum Hukuncin Daurin Rai Da Rai A Ekiti
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon-Gaba Da Jami’an Lafiya Da Marasa Lafiya A Jihar Neja
Mazauna garin sun shaida wa jaridar Leadership Hausa a ranar Talata cewa, an kashe mutanen ne a kauyen a lokacin da ‘yan bindigar suka isa wurin a kan babura suka fara harbe-harbe a ko’ina.
A cewar mazauna kauyen, maharan da suka kai farmaki kauyen da misalin karfe 9:30 na dare, sun kuma yi awon gaba da wasu ’ya’yansa biyar sannan suka hada da matansa biyu.
Wani shugaban matasa a Wase, Shapi’i Sambo, ya ce, “Maharani sun zo ne da yawansu kuma suka fara harbe-harbe.
“Sun je gidan basaraken gargajiya kai tsaye, suka kashe shi suka yi awon gaba da mutum biyar daga cikin iyalansa.
“’Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da dimbin babura na jama’ar yankin.
Kakakin Rundunar ’yansandan Jihar Filato, DSP Alabo Alfred, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an tsaro sun fara bincike kan lamarin.