An kashe jami’an tsaro 5 masu kula da al’umma (CWC) a wani mummunan harin kwantan bauna da wasu ‘yan bindiga suka kai a kauyen Maharba da ke karamar hukumar Matazu a jihar Katsina.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda a ranar Juma’ar da ta gabata ya jagoranci tawagar jami’an tsaro zuwa yankin domin ganin irin barnar da harin ya haifar.
- Tawagar MDD Da Majalisar Shugabancin Libya Sun Kafa Kwamitin Tsagaita Bude Wuta
- Shugaban Hukumar DSS Ya Kaddamar Da Cibiyar Koyar Da Addinin Musulunci A Kaduna
Jami’an da aka kashen da suka hada da Kwamandan CWC Mallam Sanusi, rahotanni sun bayyana cewa, suna cikin wani aikin kai dauki ne yayin da wasu ‘yan bindiga kusan ashirin (20) dauke da makamai a babura suka yi musu kwanton bauna a madatsar wani rafi.
A cewar wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Ibrahim Kaula ya fitar, maharan wadanda suka boye jikin bishiyar mangwaro, sun kona motar jami’an tsaro kirar Hilux a yayin harin.
Gwamna Radda ya samu rakiyar kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Dr. Nasiru Danmusa; Kwamishinan ’Yansandan Jihar, Daraktan Ma’aikata na Jihar, Shugaban Ma’aikata, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir; da sauran manyan jami’an tsaro.
Shugaban karamar hukumar, Alhaji Shamsudeen Sayaya ne ya jagoranci Radda zuwa inda harin ya faru.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai yayin ziyarar, Gwamna Radda ya yi Allah-wadai da harin, yana mai bayyana shi a matsayin “babbar rashi ga jihar,” sannan ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta kara kaimi wajen tabbatar da tsaron dukkan al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp