Wani makiyayi mai suna Hamza Sulaiman ‘, ya rasa ransa bayan da wasu ‘yan bindiga sun kai hari lokacin da wasu makiyaya ke kiwon shanu a ƙauyen Shen da ke ƙaramar hukumar Jos ta Kudu, a Jihar Filato.
Shugaban ƙungiyar Gan Allah Fulani Development Association (GAFDAN) kuma shugaban haɗakar ƙungiyoyin Fulani masu rijista, Garba Abdullahi ne, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Jos.
- Sin Ta Bukaci Amurka Ta Daina Siyasantar Da Batun Asalin Cutar COVID-19
- Gwamna Zulum Ya Ƙaddamar Da Aikin Gina Titi Da Gadar Sama Ta Huɗu A Borno
Ya ce maharan sun harbe shanu uku da tunkiya ɗaya a harin.
Shugaban ƙungiyar ci gaban yankin Du, Mista Silas Bot, ya bayyana cewa ko da akwai wata matsala da ta faru kafin hakan, hakan ba ya nufin mutane su ɗauki doka a hannunsu ba.
Ya ce akwai lokutan da makiyaya ke shiga gonakin manoma su yi kiwo, amma hakan bai zama dalilin tashin hankali ba.
Ya roƙi matasa da su zauna lafiya kuma su riƙa kai rahoton duk wani abu na barazana ga jami’an tsaro, domin nemo mafita game da hare-haren da ke ci gaba da faruwa.
Garba Abdullahi ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da makiyayan shida ke kiwo.
“Da maharan suka fara harbi, ɗaya daga cikin makiyayan da ya tsira ne ya kira ya ba mu labari. Ina samun labarin, na garzaya wani shingen sojoji da ke Latiya, inda na kai rahoto. Daga nan jami’an tsaro tare da ni muka tafi wajen, mun tarar da shanun da tumakin da aka kashe,” in ji shi.
Shugabannin ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) da GAFDAN a jihar, Ibrahim Babayo da Garba Abdullahi, sun yi kira ga hukumomin tsaro da su binciki lamarin tare da hukunta waɗanda suka aikata laifin.
Haka kuma sun roƙi mambobinsu da su zauna lafiya kuma ka da su ɗauki doka a hannunsu, su bar hukumomin tsaro su ɗauki mataki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp