Rahotanni da ke fitowa daga Jihar Zamfara sun bayyana cewar ‘yan bindiga sun kai hare-hare mabanbanta, inda suka kashe manoma 30, tare da wani malamin addinin Muslunci a jihar.
Maharan sun kai mabanbantan hare-haren ne a kauyen Gidanngoga da ke karamar hukumar Maradun da kuma kauyen Bilbis da ke karamar hukumar Tsafe a jihar.
- Gwamnan Zamfara Ya Sauke Nauyin Bashin Haƙƙoƙin Ma’aikata Na Fiye Da Naira Biliyan 4
- Yadda Bankuna Da Cibiyoyin Kudi Ke Tafka Asara Sakamakon Fara Amfani Da Fasahar Zamani Ta AI
Maharan sun fara kai farmaki karamar hukumar Maradun, inda suka kai hari kauyen Gidangoga, yayin da manoma ke kokarin gyara gonakinsu saboda karatowar damina.
Kazalika, maharan sun hallaka Malam Makwashi Maradun Mai Jan Baki, a lokacin da yake aiki a gonarsa.
Malamin ya yi fice wajen karanta Alkur’ani mai girma musamman a tafsirin watan Ramadan a Masallacin Juma’a na garin.
Har wa yau, ‘ya’yansa biyu sun bace sakamakon harin da aka kai kauyen.
Da yammacin wannan rana, ‘yan bindigar sun sake kai wani hari kauyen Bilbis da ke gundumar Tsafe, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 20.
Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewar an kai wa manoman hari ne yayin da suke gyaran gonakinsu.
An ruwaito cewa hakimin gundumar, Alhaji Murtala Ruwan Bado, ya tsallake rijiya da baya a harin da aka kai.