Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe masunta uku a garin Sanyinna da ke Æ™aramar hukumar Tangaza a Jihar Sakkwto, a wani harin da suka kai da safiyar Talata.
Wani mazaunin yankin ya ce waÉ—anda aka kashe suna kamun kifi ne lokacin da ‘yan bindigar suka kai musu hari.
- Ya Kamata Lambar Yabo Ta Zama Hanyar Ƙarfafa Mana Gwuiwa – Misis Nda-Isaiah
- ‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Satar Mota A Bauchi
A ranar Litinin kuma, ‘yan bindigar sun kai hari a wasu Æ™auyuka biyu—Sutti da Takkau—inda suka jikkata mutane biyu tare da sace dabbobi da dama kamar shanu, raÆ™uma, tumaki da awaki.
Mai bai ws shugaban ƙaramar hukumar Tangaza shawara kan harkar tsaro, Garzali Raka, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce jami’an tsaro sun mayar da martani da gaggawa, inda suka fafata da ‘yan bindigar har suka Æ™wato dabbobin da suka sace a garin Siddi.
Mutane biyun da suka jikkata na karɓar magani a Asibitin Gwamnati na Tangaza.
Raka ya buƙaci gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa don daƙile hare-haren da ke ƙara yawaita a yankin, tare da dawo da zaman lafiya domin ci gaban al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp