’Yan bindiga sun kashe mutane 22, ciki har da sojoji huɗu, a wani hari da suka kai hanyar Gwashi-Nassarawa da ke Ƙaramar Hukumar Bukkuyum a Jihar Zamfara.
Harin ya faru ne ranar Lahadi, lokacin da sojojin ke bakin aiki.
Har zuwa ranar Litinin, ba a gano gawarwakin wasu daga cikin waɗanda aka kashe ba.
A wani harin kuma, sama da mazauna ƙauyuka 400 ne suka tsere daga wasu garuruwa uku a yankin Dansadau na Ƙaramar Hukumar Maru, bayan ’yan bindiga sun kai hare-hare tare da ƙone motoci sama da 12.
Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun kuma buƙaci a biya su harajin naira miliyan 50.
A jam’iyyar NDC na Jihar Zamfara ya yi Allah-wadai da hare-haren, tare da kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar da su tura ƙarin jami’an tsaro domin kare al’ummar da ke fuskantar barazanar hare-hare.














