’Yan bindiga sun kashe mutane tare tare da yin awon gaba da wasu a wani hari da suka kai a kauyen Dan Tudu da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato.
Harin ya auku ne da sanyin safiyar ranar Litinin.
- Majalisar Dokokin Kano Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Gyaran Dokar Haraji A Nijeriya
- Peng Liyuan Ta Yi Kiran Ci Gaba Da Aiki Da Matasa Wajen Rigakafin Cutar AIDS
Yanzu haka al’ummar garin Dan tudu da ke Lajinge a karamar hukumar Sabon Birni a gabashin Sakkwato na ci gaba da jimamin mutane tara da suka rasa rayukansu.
Wani mazaunin garin da ya tsira daga harin ya shaida cewa, da ma mutanen garin sun samu labarin cewa akwai yiwuwar ‘yan bindiga na kan hanyar kai hari a garin.
Shugaban karamar hukumar Ayuba Hashimu, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Wannan dai na zuwa ne a lokacin da mahukunta a jihar ke cewa ana samun nasara a kan ‘yan bindiga.
A baya-bayan an samu rahotannin cewa, jami’an tsaro na tafka fada da ‘yan bindiga, kuma jami’an tsaro na sa-kai da ‘yan banga na kokari, wajen kawo karshe mahara a Jihar Sakkwato.