Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba a safiyar Laraba, 1 ga watan Fabrairu, sun kai hari ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC a Ojoto, karamar hukumar Idemili ta Kudu a Anambra.
‘Yan bindigar wadanda ke dauke da muggan makamai da suka hada da abubuwan fashewa da man fetur, sun kuma kai hari a ofishin ‘yan sanda da ke Nnobi, a karamar hukumar, da kuma wani ginin da ke cikin ofishin, inda suka kashe wani yaro, tare da raunata wata yarinya.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Toochukwu Ikenga, ya ce harin ya afku ne da misalin karfe 1:45 na daren ranar Laraba, inda ya tabbatar da cewa maharan sun zo da adadi mai yawa, acikin motocin Toyota Sienna guda hudu.