Kungiyar Ci gaban Masarautar Birnin-Gwari (BEPU) ta bayyana rasuwar mataimakin shugaban kungiyar Jama’atul Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus-Sunnah (JIBWIS), reshen Birnin-Gwari, Mal. Yakubu Muhammad Bugai da wasu manoma uku da wasu ‘yan bindiga suka kashe a yankin tare da yin garkuwa da mutane sama da 50.
Shugaban na JIBWIS, an harbe shi ne a ranar Larabar da ta gabata a gonarsa da ke kusa da unguwar Rema.
- Nijar: AU Ta Umarci Sojoji Su Koma Bariki Nan Da Kwana 15
- Za A Kara Kashi 10 A Kasafin Bangaren Lafiya
Har zuwa lokacin da aka kashe shi, Mal. Bugai ya kasance babban ginshiki, jagaba sannan kuma mataimakin shugaban gidauniyar marayu ta Birnin-Gwari, kungiya ce da ta dukufa wajen daukar nauyin dubban marayun da akasari ‘yan fashi da makami suka kashe wa iyaye a karamar hukumar.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar ta BEPU, Ishaq Usman Kasai ya fitar ta kuma bayyana cewa, a wani lamari mai cike da bakin ciki yadda mahara suka sace da dama a kewayen Sabon-Layi, Kurgi, Yelwa, Tashan-Keji, Shiwaka, Unguwan Danfulani da sauran al’ummomin karkara da dama a yammacin Birnin-Gwari da ke yankin.
“’Yan bindigar sun kuma sun share fiye da gonaki 10 musamman wadanda aka noma masara.
Birnin-Gwari da wasu yankuna na jihar Kaduna na ci gaba da fuskantar hare-haren ‘yan bindiga a jihar.