‘Yan bindiga dadi da ke cin karensu babu babbaka sun kashe a kalla jami’an sojoji da ‘yansanda 154 a cikin shekara daya.
Binciken LEADERSHIP ya gano cewa a tsakannin watan Maris na 2023 zuwa Maris din 2024, jami’an ‘yansanda 90 ne aka kashe, yayin da kuma jami’an sojoji su 64 suka rasa rayukansu sakamakon aikace-aikacen ‘yan bindiga dadi.
- Sin Ta Bayyana Rashin Jin Dadi Kan Binciken Da Eu Ta Yiwa Wasu Kamfanonin Sin Masu Samar Da Wasu Hajoji
- Samun Tunanin Kashin Kai Zai Tabbatar Da Damar Ci Gaba
Bugu da kari, barnar ‘yan bindigan ya kai ga shafan wasu ‘yan kungiyan Sa-kai a karamar hukumar Mariga ta Jihar Neja, inda ‘yan sa-kai mutum 30 suka rasa rayukansu.
LEADERSHIP ta iya fahimtar cewa an kafa ‘yan sa-kai ne da nufin su yaki ‘yan fash-in daji da ‘yan bindiga dadi ta hanyar yin hadin guiwa da jama’an tsaro wajen ya-kar ‘yan fashin daji a yankunansu.
Wata majiya ta ce ‘yan fashin dajin sun farmaki mambobin kungiyar ‘yan sa-kai ne wadanda suke kan aikin bin sawun ‘yan fashin daji biyo bayan da suka yi garkuwa da wasu manoma a Dogon Dawa.
Majiyar ta ce ‘yan sa-kai na kokarin bibiyar takun ‘yan bindigan ne zuwa ma-boyarsu, inda suka auka tare da da kashe 30 a cikin ‘yan sa-kan gami da jikkata wasu da dama.
Shugaban karamar hukumar Mariga, Abbas Kasuwar Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da nuna matukar damuwa dangane da cewa mazauna yankunan na kokarin tsunduma gudanar da harkokin noma sai kuma mummunar annobar kai hare-hare na neman kara jefa su cikin halin firgici.
Ya ce a baya yankin na morar zaman lafiya don haka ne ya yi kira ga gwamnati da ta yi duk mai yiyuwa wajen shawo kan matsalar tsaron da ke barazana ga yankin.
A bangaren sojoji kuwa, mummunar hare-haren sun wakana ne a watan Agustan 2023 da Maris 2024 a jihohin Neja da Delta.
Na ‘yansandan Nijeriya kuwa, babban harin da ya wakana shi ne, wanda lokacin da ‘yan bindiga dadi suka yi kwautan bauna tare da hallaka babban jami’in dan-sanda (DPO), Bako Angbanshin tare da yin gunduwa-gunduwa da gawarsa a yankin Odumude da ke karamar hukumar Ahoada ta gabas a Jihar Ribas. Sai bayan wata shida da faruwar lamarin ne aka iya gano gawarsa.
Jerin Kashe-kashen Da Aka Yi Wa ‘Yansanda a shekarar 2023
A ranar 5 ga watan Maris 2023, ‘yan bindiga dadi sun kashe dansanda da jikkata wasu biyu a Jihar Anambra.
Tsakanin ranakun 13 zuwa 18 na Maris, ‘yansanda I6 ne aka kashe a yankin Ngas-ki da Gafara a karamar hukumar Ngaski ta Jihar Kebbi, a Jihar Neja da a Jihar Imo.
A ranar 20 ga Maris, rundunar ‘yansanda ta tabbatar da cewa sojoji sun kashe mata jami’ai guda biyu a Jihar Taraba.
A ranar 26 ga Maris, ‘yan bindiga sun farmaki shingen bincike ‘yansanda, inda su-ka kashe ‘yansanda biyu a Jihar Inugu.
Ranar 6 ga Afrilu, ‘yansanda uku ne aka kashe a Edo da raunata wani guda.
Ranar 7 ga Afrilu, wasu ‘yan bindiga dadin da ba a gano su waye ba sun harbe dansanda har lahira a Marine Base Junction da ke Fatakwal.
A ranar 21 ga Afrilu, ‘yan bindiga dadi sun kashe jami’an ‘yansanda biyar a Jihar Imo.
A ranar 26 ga watan Afrilu, wasu da ake zargin ‘’yan Yahoo boy’ ne sun kashe dansanda a Ibadan.
A ranar 28 ga watan Afriku, dansanda, Sergeant Ifeanyi an kasheshi bayan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi a Jihar Delta.
Ranar 3 ga Mayu, ‘yan bindigan sun fille kan wani mataimakin sufuretandan dan-sanda da aka bayyana sunansa da Linus a kan layin East da ke Ndiegoro a Aba ta Jihar Abiya.
A ranar 16 ga watan Mayu, ‘yansanda biyu ne aka kashe a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari ga tawagar jami’an Amurka a Anambra.
Ranar 20 ga Mayu, ‘yan bindiga sun harbe ‘yansanda biyu a Imo. A wannan rana, an rawaito cewa jami’an ‘yansanda biyu ne aka kashe a Ughelli a karamar huku-mar Ughelli ta arewa a Jihar Delta a wani barin wuta, yayin da wani ya jikkata.
A ranar 24 ga May, harbin ‘yan bindiga dadi ya kashe wani dansanda a Ebonyi.
A ranar 18 ga watan Yuni, dansanda daya ne ya rasa ransa a lokacin da ‘yan bin-diga suka farmaki tawagar tsohon gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha a Jihar Imo.
Ranar 26 ga Yuli, rundunar ‘yansanda ta tabbatar da cewa an kai hari ga tawagar kwamishina har an kashe jami’an ‘yansanda biyu a Aba.
A ranar 23 ga Yuli, wasu da ake zargin ‘yan fashin daji ne sun kai hari ga jami’an ‘yansanda a lokacin da suke bakin aikin tsaida mutane domin bincike a shata-letalen Oleh da ke Jihar Delta, inda suka kashe ‘yansanda biyu tare da banka wa motarsu ta sintiri wuta.
A ranar 11 ga Agustan, ‘yan acaba sun dira kan wani dansanda, inda suka kasheshi a Legas.
A ranar 25 ga Agustan, ‘yan bindiga sun kashe jami’in dansanda mai mukamin sufeto tare da yin awun gaba da bindigarsa a Ribas.
A ranar 8 ga Sabumba ne ‘yan bindiga suka kai hari tare da kashe wani DPO, Bako Angbanshin a yankin Odumude da ke karamar hukumar Ahoada ta gabas a Jihar Ribas.
Ranar 19 ga Satumba, akalla ‘yansanda biyar ne aka kashe a wani harin da ‘yan bindiga suka kai musu a kudancin Jihar Imo.
Ranar 20 ga Satumba, wasu ‘yan bindiga sun hallaka jami’an ‘yansanda biyu a ji-har Inugu.
A ranar 14 ga Oktoba, ‘yan fashi da makami sun kashe jami’in dansandan Nijeriya mai suna Joseph Fidus a gidansa da ke Iyana Cele a yankin Sango ta Jihar Ogun.
A ranar 21 ga Oktoba, ‘yan fashin banki sun hallaka ‘yansanda hudu a Jihar Benu-wai.
Ranar 27 ga Oktoba, ‘yan bindiga dadi sun kashe ‘yansanda biyu a lokacin da suke kokarin yin wani kame a Aba.
Ranar 17 Nuwamba, ‘yan daba sun kashe ‘yansanda biyu da jikkata wani guda a Jihar Ebonyi.
A ranar 18 ga Nuwamba, ‘yansanda biyu ne suka bakwanci lahira a wani harin da ake zargin cewa mambobin IPOB ne suka aiwaar a shalkwatar ‘yansanda da ke Ebonyi.
Ranar 22 ga Nuwamba, an zargi wani jami’n soja da kashe wani jami’in dansanda a wani caji ofis din ‘yansanda da ke Jihar Adamawa.
A ranar 27 ga Nuwamba, wasu ‘yan bindiga dadi da ba a san ko su waye ba sun kashe ‘yansanda biyu a Ahaira Junction da ke karamar hukumar Ahaizu Mbaise a Jihar.