Al’ummar Æ™ananan hukumomin Shiroro, Muya, da Rafi a Jihar Neja sun koka kan yadda ‘yan bindiga daga Birnin Gwari, a Jihar Kaduna, ke kutsawa yankunansu domin aikata ta’addanci tun bayan sulhun da aka yi tsakanin gwamnatin Kaduna da ‘yan bindigar.
Mazauna yankin sun bayyana cewa hare-haren sun ƙaru, ciki har da sacw mutane don neman kuɗin fansa.
- Abubuwan Dake Kunshe Cikin Rahoton Shekara-Shekara Game Da Cinikin Shige Da Fice Na Kasar Sin
- An Samu Adadin Shige Da Fice Miliyan 610 a Kasar SinÂ
Alhaji Usman daga Shiroro ya ce a jiya kawai, ‘yan bindiga sun kutsa Æ™auyen Afaka, inda suka sace mutane 20.
Malam Muhammadu daga Rafi ma ya ce lamarin ya tsananta, yana haifar da zaman zulumi a yankin.
Gwamnan Neja, Umar Muhammed Bago, ya bayyana cewa gwamnatinsa na É—aukar matakan tsaro domin daÆ™ile hare-haren kuma tana shirye ta yi sulhu da ‘yan bindigar domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
A baya dai yankin Shiroro ya fuskanci hare-hare daga mayaƙan Boko Haram, waɗanda suka kafa sansani a dajin yankin.