Wasu ‘yan bindiga sun kone gonaki 20 na masara da waken suya da dawa a Karamar Hukumar Kontagora da ke Jihar Neja.
Daya daga cikin manoman da aka kone gonakinsu, ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun kuma ajiye musu wata wasikar gargadi, inda suka bukaci kowanne manomi ya biya su Naira miliyan 30 ko kuma su fuskanci farmaki.
- Kasar Sin Ta Bukaci Kasa Da Kasa Su Mara Baya Wajen Kawar Da Makaman Nukiliya Daga Gabas Ta Tsakiya
- Kwararre Dan Kasar Croatia : “Double 11” Ya Nuna Juriyar Tattalin Arzikin Kasar Sin
‘Yan bindigar sun ajiye lambar wayar da za a kira su, kuma tuni wasu daga cikin manoman suka tuntube su, inda suka shaida musu cewa, lallai su ne suka kone musu gonaki, sannan suka yi musu barazanar daukar mataki.
Yanzu haka wadannan manoma na rokon gwamnatin tarayya da ta jihar da su kai musu agajin gaggawa.
‘Yan bindigar sun kone albarkatun gonar ne da suka isa girbi kamar yadda manoman suka bayyana, yayin da suke shirye-shiryen kawo abincin da suka noma gidajensu don ciyar da iyali amma hakan bai yiwuwa ba saboda harin.
Jihar Neja dai na daya daga cikin jihohin da ke ci gaba da fuskantar matsin lambar hare-hare daga ‘yan ta’adda.