An yi garkuwa da kwamishinan yada labarai, al’adu da yawon bude ido na jihar Nasarawa, Mallam Yakubu Lawal.
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi garkuwa da Lawal daga gidansa da ke Nasarawa Eggon a daren ranar Litinin bayan harbe-harbe da ‘yan bindigan suka yi.
Wata majiya mai tushe da ta so a sakaya sunanta ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ‘yan bindigar da suka sace Kwamishinan suna dauke da muggan makamai.
Kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta ci tura a lokacin da ake kokarin hada rahoton.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp