Ana zargin ‘yan bindiga da sace kwararren likitan mata, Dokta Abidemi Oyaromade a Jihar Zamfara.
‘Yan bindigar sun kai hari gidan likitan da ke yankin Mareri a garin Gusau, Jihar Zamfara, da sanyin safiyar Litinin tare da yin awon gaba da shi.
- Sanata Sani Ya Nemi Tinubu Ya Saki Masu Zanga-zanga Da Ke Tsare
- An Yi Bikin Murnar Cikar Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Jihar Xinjiang Shekaru 70 Da Kafuwa
An ce ‘yan bindigar sun kai farmakin da misalin karfe 4 na safe sannan suka sace shi.
Dokta Oyaromade ya taba zama Shugaban Ayyukan Lafiya a Asibitin Kwararru na Ahmad Sani Yariman Bakura da ke Gusau daga 2016 zuwa 2017.
Ya kuma ya ci gaba da aiki a asibitin har zuwa karshen shekarar 2023 kafin ya koma Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Gusau.
Wata majiya mai tushe, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ya ce ya tuntubi iyalan Dokta Oyaromade ta waya, kuma sun tabbatar masa da sace likitan.
An ce Shugaban Kungiyar Likitoci ta Nijeriya (NMA), na jihar ya halarci wani taro, kuma mai yiwuwa yana da alaka da sace likitan.
Rundunar ‘yansandan Jihar Zamfara ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba tukuna.