Mazauna kauyen Tsamiya da ke karamar hukumar Shanono ta jihar Kano sun sake fuskantar hari yayin da ‘yan bindiga suka sace wasu mutane 11, ciki har da wata mai shayarwa, a wani sabon hari da suka kai wa al’ummar.
Shugaban Kwamitin Tsaro na Al’ummar Faruruwa, Yahaya Bagobiri, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa maharan sun mamaye kauyen da yawa a yammacin Lahadi.
- Sultan Ya Nemi Gwamnonin Arewa Da Su Riƙa Saurarar Masu Sukarsu
- Jakadan Bangladesh Ya Yaba Wa MAAUN, Ya Buƙaci A Kafa Reshen Jami’ar A Ƙasarsa
Ya ce ‘yan bindigar suna zirga-zirgar su hankali kwance ba tare da wata fargaba daga jami’an tsaro ba har suka tafi da mutane duk da sanarwar da aka bayar da wuri ga jami’an tsaro a yankin.
A cewar Bagobiri, mazauna kauyen sun sami sahihan bayanai kan tahowar ‘yan bindigar awanni kafin harin, wanda hakan ya sa suka sanar da jami’an tsaro amma suka ce ba a ba su izinin zuwa ba.
“Tun daga misalin karfe 7 na yamma, mun ji labarin cewa ‘yan bindigar suna tahowa zuwa al’ummarmu. Mun ji cewa an gan su a kusa da Kogari kuma suna ci gaba da tafiya. Nan da nan muka sanar da hukumomin tsaro, amma suka ce ba a ba su umarnin zuwa ba,” in ji shi.
Duk kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta cutura saboda layin wayarsa yana kashe lokacin haɗa wannan rahoto.














