Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Kaura Namoda/Birnin Magaji a Jihar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya ce ’yan bindiga sun yi garkuwa da sama da mutane 200 a yankinsa.
Yayin da yake zantawa da manema labarai a a ranar Laraba, Jaji ya bayyana cewa matsalar tsaro a mazaɓarsa na ƙara ƙamari, inda ya yi kira ga gwamnati ta gaggauta ɗauki mataki.
- ASUU Ta Yi Barazanar Maka JAMB A Kotu Biyo Bayan Samun Mummunan Sakamako A UTME
- Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha
Ya bayyana cewa cikin makonni biyu da suka gabata, ’yan bindiga sun sace mutane 60 a garin Banga.
Daga bisani sun kashe 10 daga cikinsu saboda ‘yan uwansu sun gaza tara kuɗin fansa Naira miliyan 30 da maharan suka buƙata ba.
Ya ƙara da cewa kafin su gama jimamin wannan, wasu mutum 25 kuma aka sake sace su a ƙauyen Gabake.
A ranar Talata ma, an sake kai hari a ƙauyen Kungurki.
Jaji, wanda ya taɓa zama Shugaban Kwamitin Tsaro da Leƙen Asiri a Majalisar Wakilai ta 8, ya ce bai dace a ayyana dokar ta ɓaci a Zamfara kaɗai ba, ganin cewa sama da jihohi 20 na fama da irin wannan matsalar.
“Ina ganin idan za a ayyana dokar ta ɓaci a Zamfara, to ya kamata a yi hakan a wasu jihohi sama da 20. Matsalar tsaro ta zama ta ƙasa baki ɗaya, ba na yanki guda ba. Wannan ba siyasa ba ce. Idan ba mu ɗauki mataki yanzu ba, lamarin na iya shafar ƙasa gaba ɗaya,” in ji shi.
Dangane da kiraye-kirayen amfani da dakarun haya daga ƙasashen waje domin yaƙi da ta’addanci, Jaji ya ce bai goyi bayan hakan ba.
Ya ce dakarun Nijeriya suna da ƙarfin da zai iya magance matsalar, muddin aka tallafa musu yadda ya kamata.
“Bai kamata mu nemi dakarun haya ba. Abin da muke buƙata shi ne a bai wa dakarunmu kayan aiki na zamani da kuma kulawa ta fuskar walwala. Idan aka ba su goyon baya da kayan aiki masu kyau, za su iya shawo kan ’yan ta’adda,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp