‘Yan bindiga sun sace mutum bakwai, ciki har da wata matar aure, a wani hari da suka kai da daddare garin Kontagora, a Jihar Neja.
Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa harin ya faru ne da daren ranar Lahadi a gidajen da ke wajen garin.
- Gidauniyar Dangote Ta Bai Wa Jihar Bauchi Tallafin Buhun shinkafa 25,000
- Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Kwamishinan Ganduje Kan Zargin Ɓatan N240m
Yankunan da abin ya shafa sun haɗa da rukunin gidaje na Talba, Rafin Karma, Dadin Kowa, Gangaren-Sagi, da Kontagora bypass.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka sace ita ce wata mata da mijinta ya tsere.
Amma har yanzu ba a san inda ta ke ba.
Wani mazaunin yankin ya koka da yadda ‘yan bindiga ke yawan kai hare-hare a waɗannan wurare, lamarin da ya sa jama’a ke cikin fargaba.
A Farin-Shinge, mazauna yankin sun nuna koka kan hare-haren da ke ci gaba da faruwa, inda suka roƙi gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki matakin gaggawa.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da harin kuma ya ce za su binciki lamarin.
Sai dai, har zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoto, ba a samu ƙarin bayani daga ‘yansanda ba.