ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Kwamishinan Ganduje Kan Zargin Ɓatan N240m

by Sadiq
1 year ago
Ganduje

Babbar Kotun Jihar Kano, ta bayar da umarnin kama Barista M. A. Lawal, tsohon Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’a, bayan ya gaza halartar kotu domin gurfana kan tuhume-tuhume da ake masa.

Ana tuhumar Lawal da laifuka huɗu da suka shafi ɓatan da kuɗi da kuma cin amana da suka kai Naira miliyan 240.

  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [10]
  • Ga Dukkan Alamu Kaikayi Zai Koma Kan Mashekiya

Shari’ar tana kuma shafar Abdullahi Umar Ganduje, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano.

ADVERTISEMENT

A zaman kotun na ranar Litinin, masu gabatar da ƙara sun sanar da kotu cewa har yanzu ba a miƙa wa Ganduje sammaci ba, duk da umarnin da aka bayar a baya.

Sai dai an aike wa Lawal sammaci amma bai bayyana a kotu ba.

LABARAI MASU NASABA

Wasikar Trump Ba Za Ta Taimaki Tinubu Ya Lashe Zaɓen 2027 Ba – ADC

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma Sama Da 20 A Zamfara – Amnesty International

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu, ta bayar da umarnin kama Lawal tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Mayu.

A wata shari’a daban, kotun ta kuma bayar da umarnin kama Jibrilla Muhammad, tsohon Manajan Darakta na Kamfanin Zuba Jari da Kadarorin Kano (KSIP), bisa zargin ɓatan Naira miliyan 212.4.

A gefe guda ta sake ɗage zaman wannan shari’a saboda abokin shari’ar tasa, Dauda Sheshe, har yanzu bai karɓi sammaci ba.

An ɗage shari’arsu zuwa ranar 29 ga watan Afrilu.

Dukkanin waɗannan shari’u na da alaƙa da zargin karkatar da kuɗaɗen jama’a yayin da suke rike da muƙaman gwamnati.

MASU ALAKA

Wasikar Trump Ba Za Ta Taimaki Tinubu Ya Lashe Zaɓen 2027 Ba – ADC
Manyan Labarai

Wasikar Trump Ba Za Ta Taimaki Tinubu Ya Lashe Zaɓen 2027 Ba – ADC

July 23, 2026
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma Sama Da 20 A Zamfara – Amnesty International
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma Sama Da 20 A Zamfara – Amnesty International

July 23, 2026
Sojoji Sun Daƙile Harin ISWAP,  Sun Kashe ’Yan Ta’adda 20 A Yobe
Manyan Labarai

Rashin Tsaro: Tinubu Ya Amince Da Kafa Sabuwar Bataliyar Sojoji A Jihar Kwara

July 23, 2026
Next Post
Kotu Ta Dakatar Da Majalisar Dokokin Ribas Daga Tsige Fubara

Rikicin Ribas: Zarge-zargen Da Majalisa Ke Yi Wa Gwamna Fubara

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Amurka Na Neman Ra’ayoyi A Kan Shirin Rage Haraji

Sin Da Amurka Na Neman Ra’ayoyi A Kan Shirin Rage Haraji

July 23, 2026
Binciken CGTN: Ya Kamata Kasashen Tekun Kudancin Sin Su Rike Ragamar Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankalin Yankin A Hannunsu

Binciken CGTN: Ya Kamata Kasashen Tekun Kudancin Sin Su Rike Ragamar Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankalin Yankin A Hannunsu

July 23, 2026
Radda Ya Ƙaddamar Da Sabbin Ayyuka, Ya Kara Tallafa Wa Ƙananan ’Yan Kasuwa A Katsina

Radda Ya Ƙaddamar Da Sabbin Ayyuka, Ya Kara Tallafa Wa Ƙananan ’Yan Kasuwa A Katsina

July 23, 2026
Wadanne Dalilai Ne Suke Sabbaba Karin Karbuwar Sin Tsakanin Al’ummun Duniya?

Wadanne Dalilai Ne Suke Sabbaba Karin Karbuwar Sin Tsakanin Al’ummun Duniya?

July 23, 2026
Ƙasashen Yankin Sahel 3 Sun Nuna Sha’awar Karɓar Bakuncin Gasar AFCON Ta 2032

Ƙasashen Yankin Sahel 3 Sun Nuna Sha’awar Karɓar Bakuncin Gasar AFCON Ta 2032

July 23, 2026
Sin Ta Kaddamar Da Shirin Shekaru Biyar Na Bunkasa Makamashi Da Ake Iya Sabuntawa  

Sin Ta Kaddamar Da Shirin Shekaru Biyar Na Bunkasa Makamashi Da Ake Iya Sabuntawa  

July 23, 2026
Wasikar Trump Ba Za Ta Taimaki Tinubu Ya Lashe Zaɓen 2027 Ba – ADC

Wasikar Trump Ba Za Ta Taimaki Tinubu Ya Lashe Zaɓen 2027 Ba – ADC

July 23, 2026
An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 25 Da Daddale Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Da Sada Zumunta A Tsakanin Sin Da Rasha

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 25 Da Daddale Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Da Sada Zumunta A Tsakanin Sin Da Rasha

July 23, 2026
Wang Yi Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio

Wang Yi Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio

July 23, 2026
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma Sama Da 20 A Zamfara – Amnesty International

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma Sama Da 20 A Zamfara – Amnesty International

July 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.