Wasu ‘yan bindiga sun sace shugaban jam’iyyar APC na mazaɓar Ifon ta 5, Hon. Nelson Adepoyigi a ƙaramar hukumar Ose a Jihar Ondo.
An sace shi ne da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Litinin, yayin da yake ƙoƙarin ajiye motarsa.
- Rikicin Ribas: Fubara Ya Ce Ya San Yadda Zai Magance Matsalar, Ya Gargaɗi Magoya Bayansa
- Bam Ya Hallaka Ma’aikatan Hukumar Ilimi 2 A Hanyar Damboa-Maiduguri
Wata majiya ta ce maharan sun shiga gidansa, suka dinga dukansa da sanda kafin su tafi da shi.
Matarsa ta ji lokacin da yake ihu yake neman agaji, amma kafin ta fito, maharan sun tafi da shi.
Maharan sun tuntuɓi iyalinsa inda suka nemi a biya su Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa kafin sakin sa.
Kwamandan rundunar Amotekun a Jihar Ondo, Adetunji Adeleye, ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce ana ƙoƙarin ceto Adepoyigi.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Ondo, Olushola Ayanlade, shi ma ya tabbatar da sace shugaban na APC, inda ya ce an sace shi a gonarsa da ke hanyar Ifon-Owo.
Ya ƙara da cewa DPO na Ifon tare da mafarauta, ‘yan sa-kai da sojoji sun fara bincike domin gano inda aka kai shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp