Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum na jihar Zamfara, Suleiman Abubakar Gumi, ya ce ‘Yan bindiga sun tashi sama da garuruwa 30 a cikin wannan watan na Yuni.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da kudiri kan bukatar sojoji su tura karin dakaru zuwa yankunan da abin ya shafa a jihar domin dakile hare-haren da ke kara ta’azzara.
- Gwamnan Zamfara Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Kisa Ga Masu Kai Wa ‘Yan Bindiga Rahoto
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Matar Shugaban NULGE Reshen Zamfara Mai Dauke Da Juna Biyu
Gumi ya ce a baya-bayan nan, ‘yan bindiga sun kai hari a wasu yankunan jihar, inda suka kashe mutane 16, suka jikkata wasu da dama, sun yi awon gaba da shanu da lalata dukiyoyi tare da kona ofisoshin ‘yan sanda da kuma abinci.
A cewarsa, babu wata rana da za ta wuce ba tare da kai hari a yankin ba.
Ya ce mazauna kauyuka kusan 71 sun bar gidajensu; yayin da manoma suka yi watsi da gonakinsu domin tsira.
Ya ce ‘yan fashin sun sanya haraji kan al’ummar yankin tare da neman kudin fansa daga wadanda suka yi garkuwa da su.
Hakazalika, ‘yan bindiga sun bayar da sanarwar barin kauyukan Sabon Zama, Gindin Dutse, Anguwan Tsohon Soja, Anguwar Yuhana da Anguwan Mangu da ke karamar hukumar Wase a jihar Filato.
Pinau, wani ƙauye mai nisan kilomita 11 daga Wase, ƙauyukan sun kewaye shi.
Mazauna yankin sun ce wasu ‘yan bindiga da suka rufe fuska sun afkawa mutanen yankin, inda suka bukaci ko dai su fice nan da kwanaki biyar ko kuma su fuskanci tashin hankali.
Ubale Pinau, wani mazaunin garin Pinau, ya shaida cewa ‘yan bindigar sun yi barazanar kai hari a yankin, inda ya shawarce su da su fice idan ba haka ba su fuskanci abin da zai biyo baya.
Ya ce mutane da dama sun fara tururuwa zuwa Pinau da sauran manyan garuruwa domin tsira.
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘Operation Safe Haven’ Manjo Ishaku Takwa, ya ce bai san da sanarwar sallamar ba.