Rahotanni daga ƙananan hukumomin Tsafe da Bukkuyum na Jihar Zamfara, sun nuna cewa ‘yan bindiga sun ɗora wa mutanen yankunan haraji mai yawa, wanda ya kai kusan Naira miliyan 200, tare da neman ba su buhunan abinci da kayan masarufi.
A ƙaramar hukumar Tsafe, ‘yan bindigar karkashin jagorancin shugabansu, Ɗan-Isuhu, sun buƙaci al’ummar garuruwan Gijinzama, Dakolo, Gunja, Kane, da Kurar Mota su biya haraji mai tsada, inda suka raba harajin kamar haka:
- Yadda Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Wasu Sassa A Makkah
- Kasar Sin Ta Kara Yawan Daruruwan Jiragen Kasa A Sabon Tsarinta Na Sufurin Jiragen Kasa
- Gijinzama: Naira miliyan 8.5
- Dakolo: Naira miliyan 5 da buhunan wake 20
- Gunja: Naira miliyan 7
- Kane: Naira miliyan 5
- Kurar Mota: Naira miliyan 6
Hakazalika, al’ummar Kunchin Kalgo an tilasta su biya haraji mafi yawa na Naira miliyan 20, yayin da mutanen Sungawa da Rakyabu za su biyan Naira miliyan 15 kowannensu.
A Bukkuyum kuwa, ‘yan bindigar sun afka wa ƙauyen Ganau, suka ƙone gidaje sannan suka yi garkuwa da mutane sama da 40, galibinsu mata da yara ƙanana.
Wannan ya tilasta wa ɗaruruwan mutane barin gidajensu cikin tsoro da firgici.
Sai dai har yanzu babu wani bayani daga rundunar ‘yansandan jihar game da lamarin.
Sai dai kakakin gwamnan jihar, Mallam Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa hare-haren ‘yan bindigar sun nuna cewa suna cikin matsin lamba daga hare-haren da jami’an tsaro ke kai musu.
Wannan lamari na faruwa ne a daidai lokacin da hare-haren ‘yan bindiga ke ƙaruwa a sassan Jihar Zamfara, musamman tun bayan barazanar Bello Turji, ƙasurgumin ɗan bindiga ya yi, cewa zai ci gaba da kai farmaki muddin ba a sako ‘yan uwansa da ke tsare ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp