Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi wa dakarun bataliya ta 35 kwanton bauna a Jihar Katsina, inda suka kashe sojoji biyu, yayin da wasu hudu suka samu raunuka.
Wata majiya mai tushe, wacce mazaunin unguwar Shimfida ne, inda lamarin ya faru, ta bayyana cewa an kashe ‘yan bindiga da dama a arangamar yayin da wasu suka tsere da raunukan bindiga.
- Jami’an KAROTA Sun Cafke Tirela Makare Da Giya A Kano
- Ba A Kai Wa Kwankwaso Hari A Kogi Ba – Kungiyar Yakin Zaben Kwankwaso
Wata majiyar kuma wadda dan asalin garin Jibia ne, ta ce wani jirgin soji mai dauke da makamai, yana raka ‘yan kasuwar yankin zuwa kauyen Gurbi a lokacin da suka taka wani abu mai fashewa da ‘yan ta’addar suka binne.
Ya ce, “Nan da nan ne motar ta taka bam din, ta fashe, ‘yan bindigar suka fara harbin sojoji.
“Saboda sojoji suna da yawa, su ma suka fara harbin kan mai uwa da wabi. Dan uwana yana cikin wadanda suka je Gurbi don yin kasuwanci, kuma an ceto shi.”
Ya kara da cewa tuni mazauna garin Shimfida suka tsere zuwa garin Jibia domin samun mafaka.
Harin na zuwa ne ‘yan makonni kadan da aka mayar da mutanen Shimfida gida bayan da ‘yan bindig suka kore su daga yankin sama da watanni shida.