Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da wani hari da ‘yan bindiga suka kai a garin Safana inda suka raunata mutane uku, mutum biyu daga cikin jami’an tsaro.
Kakakin rundunar ‘yansanda na jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ne ya tabbatar da haka ga wakilin LEADERSHIP HAUSA a Katsina.
- Rashin Tsaro: Gwamnatin Katsina Za Ta Fara Bai Wa Malamai Da Masu Unguwanni Alawus
- Rashin Tsaro: Gwamnatin Katsina Ta Kaddamar Da Matasa ‘Yan Sa-Kai
Aliyu, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun so mamaye garin na Safana a cikin dare da misalin karfe 6:00 na maraice inda suka zo ne da muggan makamai suka fara harbi kan mai uwa da wabi.
Sai dai a cewar sa, baturen ‘yan sanda na Safana ya shirya wata tawaga ta jami’an tsaro inda suka fatataki ‘yan bindigar daga garin Safana.
“A lokacin wannan ɗauki ba daɗi da ‘yan bindiga sun raunata jami’anmu guda biyu tare da wani mutum ɗaya wanda yanzu haka suna asibiti ana ba su kulawa ta musamman ‘ inji shi
Ya ƙara da cewa tuni jami’ansu, suka bazama domin kamo waɗanda suka kai wannan hari. Kuma tuni an fara bincike a kan lamarin.
A nasa ɓangaren, ɗan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar ƙaramar hukumar Safana wanda shi ne mataimakin kakakin majalisar Hon. Abduljalal Haruna Runka, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Honarabul Abduljalal Runka wanda ya ce ya zuwa yanzu komai ya lafa, sai dai ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun halaka ‘ yan bindiga da dama wanda sai nan gaba za a ji yawansu.
” Yanzu nan maganar da nake da kai, mun samu labarin cewa an yi wa ɓarayin daji ɓarna sosai, kuma hakan ya faru ne saboda jajircewar jami’an tsaro da kuma dakarun tsaro na ‘Community Watch Corps’
A cewarsa, babu labarin kashe ko mutum ɗaya, sannan ba su yi nasarar sace kowa ba, sai dai sun kutsa kai cikin wani shagon sayar da magunguna sun kwashe masa ciniki.
Kamar yadda Honarabul Abduljalal Runka ya tabbatarwa manema labarai, ya ce, ‘yan bindigar sun zo ne a kan mashina akalla talatin, amma a cikin ikon Allah jami’an tsaro sun fatatake su.