Babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya bayyana cewa fiye da 60,000 daga cikin 120,000 na Boko Haram da suka mika wuya ga sojojin Nijeriya, yara ne.
Janar Musa ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na ‘Arise News’ a ranar Litinin, kuma wakilinmu ya sa ido.
- Hukumar CDC Ta Karyata Barkewar Sabbin Cututtuka Masu Yaduwa A Sin
- Gwamnan Zamfara Ya Jajanta Wa Iyalan Da Harin Jirgin Sojoji Ya Rutsa Da Su
Ya bayyana cewa, maharan sun mika wuya ne sakamakon nasarar da sojoji suka yi na datse yadda suke samun kayayyakin tallafi da suka haɗa da abinci da kuɗaɗe.
“Ba a kama ‘yan ta’adda 120,000 ba; sun mika wuya ne domin mun iya hana su samun wasu abubuwa kamar kuɗi da abinci. Mun nuna musu cewa, su ‘yan ƙasa ne kuma ana buƙatarsu in sun ajiye makamansu.”