Shugaban rundunar tsaro, Janar Lucky Irabor, ya bayyana cewa, ‘yan kungiyar Boko Haram sun hallaka mutane sama da 100,000 tare da raba mutane sama da miliyan biyu daga muhallansu.
Irabor, wanda ya sanar da hakan a Abuja a yayin rufe taron yin nazari kan kokarin da ma’aikatun gwamnatin tarayya suka yi a shekarar 2022, ya ce, ayyukan na ‘yan ta’addan, ya janyo wa Nijeriya asarar naira tiriliyan 24.
Sai dai, Irabor ya bayyana cewa, a yanzu ana kan samun nasara wajen yakar ‘yan ta’addan, duk da cewa, wasun su, na yin kaura zuwa yankin Arewa maso yamma.
A cewar Irabor, an ware wa rundunar sojin naira tiriliyan 2.5 daga cikin kasafin kudi a cikin shekaru bakwai da suka wuce, musamman domin a kara wanzar da kyakkyawan tsaron cikin gida.
Sai dai janar Irabor ya yi takaici kan yadda kudaden da rundunar ta karba ba su wuce kashi 35 a cikin dari ba.