Wasu ‘yan daba sun kashe wata dalibar kwalejin ilimi (COE) da ke Billiri a karamar hukumar Billiri da ke jihar Gombe a ranar Litinin.
Wannan lamarin na zuwa ne kasa da mako guda da wasu ‘yan daba suka kashe wata dattijowa ‘yar shekara 58 a unguwar Jekadafari da ke jihar Gombe.
- An Kwato Bindiga AK47 Guda 150 A Minna Bayan Artabu
- NFF Ta Sanar Da Ranar Fara Gasar ‘Federation Cup’ Ta Nijeriya
LEADERSHIP ta labarto cewa wadannan abubuwan na faruwa ne kasa da watanni uku da wasu ‘yan daba suka kashe fitaccen malamin addini a jihar Sheikh Albani Kuri.
Kisa na biyu shi ne wanda ya faru a ranar Juma’a a unguwar Jekadafari inda ake zargin ‘yan daban sun kashe dattijowar tare da yin awun gaba da wayarta, kana na baya-bayan nan shi ne kisan da aka yi wa dalibar kwalejin a Billiri.
Kodayake, rundunar ‘yansandan jihar ta sanar da cafke wadanda take zargi da kisan dattijowa ‘yar shekara 58, sai dai wadanda suka kashe babban malamin har yanzu ba a kai ga riskarsu ba.
Dalibar kwalejin da aka kashe mai suna Yosi Yusuf tana matakin karatun aji 2 na neman kwarewa a bangaren neman ilimin koyarwa (NCE), a cewar majiyarmu.
Wasu sun yi zargin cewa ‘yan daban sun yi wa dalibar fyade kafin daga bisani suka hallakata.
Amma, a hirarmu da daya daga cikin makwabcin mamaciyar wanda suke rayuwa a gida daya da ita, Mustapha Mohammed, ya ce, lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:50am
Ya kara da cewa sun jiyo ihunta a lokacin da suka fito domin su ga meke faruwa da ita sai suka tarar tana ta zubar da jini yayin da kuma wadanda suka tafka aika-aikar sun tsere.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Gombe, DSP Mahid Muazu Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin,