Wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kai hari tare da raunata wata tsohuwa mai shekaru 60 mai suna Safiya Yunusa, da ke zaune a Yelwa, Ƙaramar Hukumar Toro a jihar Bauchi, inda har ta kai ga ta rasa ranta.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan barandar sun kutsa kai cikin gidan Safiya da muggan makamai tare da yi mata rauni a kanta, inda aka garzaya da ita zuwa babban asibitin Toro, domin kula da lafiyarta amma da isarsu likitoci suka tabbatar da mutuwarta bayan an yi mata gwaje-gwaje.
- An Aike Ɗan Shekara 67 Gidan Yari Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Mata 2 Fyaɗe Yana Ba Su ₦500 A Bauchi
- An Ɗage Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Bauchi
Kakakin rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa a ranar Litinin, ya ce an bayar da gawar Dattijuwa Safiya ga ‘yan uwanta domin yi mata suttura, kuma tuni sun kama wani mutum da ake zargi mai suna Adamu Alhassan, mai shekaru 30 kan wannan aika-aikar.
Kakakin rundunar ‘Yansandan ya ce kamen mutumin da ake zargin ya biyo bayan bin sawunsa a wurin da abun ya faru, kuma an samu nasarar gano makamin da ake zarginsa da aikata laifin.