Wani mummunan lamari ya afku a garin Lubo, da ke ƙaramar hukumar Yamaltu-Deba, ta jihar Gombe, a safiyar yau Litinin, inda wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne suka kashe wani limamin coci, Rabaren Bala Galadima.
Marigayi Galadima, shi ne babban limami na cocin ‘Evangelical Church Winning All’ (ECWA), da ke yankin Lubo, kafin wadannan miyagu su kai masa hari tare da kashe shi a gidansa.
- ‘Yansanda Sun Kubutar Da Wata Mata Da Aka Yi Garkuwa Da Ita A Otal Din Abuja
- An Tura Manyan Injuna Domin Shiga Aikin Ceto A Lardin Sichuan
Da yake Allah wadai kan kisan, gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ta bakin mai magana da yawunsa, Isma’ila Uba Misilli, ya yi tir da mummunar aika-aikar, yana mai bayyana shi a matsayin barazana ga zaman lafiyar da jihar ke morewa.
Gwamna Inuwa Yahaya, ya kuma umarci hukumomin tsaro da su bi sawun waɗanda suka aikata wannan aika-aika domin kamu su, kana ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin da cocin ECWA, da ɗaukacin al’ummar Kirista, yana mai addu’a ga mamacin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp