Wasu ‘yan fashi da makami sun kai farmaki bankin UBA, Zenith da First Bank da ke Ankpa a jihar Kogi a ranar Laraba, inda suka yi awon gaba da wasu kudade da ba a tantance Adadin su ba.
‘Yan fashin wadanda adadinsu ya kai 20, an ce sun shigo yankin ne da misalin karfe biyu na rana, Inda suka fara da bankin UBA sannan Zenith sai kuma FirstBank na karshe.
Wani ganau ya ce ‘yan fashin sun isa yankin ne a cikin kananan motoci da bas da kuma babura.
Ganau din, ya ce bayan sun yi wa bankuna da ma’aikatan POS da ke kusa da su fashi na kusan sa’a guda, ‘yan bindigar sun fita daga garin Ankpa, suna harbe-harbe a sama.
Ba a san adadin mutanen da suka kashe ba ya zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoton.
Wani mazaunin garin ya shaida wa Daily trust cewa bayan ‘yan fashin sun wuce ne sai tawagar jami’an tsaro suka iso zuwa yankin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, SP William Aya, bai amsa waya ko sakon waya ba a lokacin hada wannan rahoton.