A ranar Talatar da ta gabata ne shahararren Jarumin nan na cikin shirin kwana Casa’in UMAR YAHAYA MANUMFASHI, wanda aka fi sani da UMAR BANKAURA ko kuma KA FI GWAMNA cikin shirin Kwana Casa’in, Allah ya karbi rayuwar bawansa, inda aka kaishi a ranar Laraba misalin karfe Tara na safe a unguwar Hotoro.
Fitaccen Jarumin da ya shafe tsahon shekaru Talatin da takwas zuwa da tara cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, bayan fina-finai na dabe da ya fara yi da su. Jarumin ya rasu ne ya bar iyalansa bayan doguwar jinya da ya sha.
- Mutane 8 Sun Mutu, 2 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kogi
- NIS Reshen Jihar Bayelsa Ta Yi Shirin Tunkarar Zaɓen 2023
Wakiliyar mu RABI’AT SIDI BALA ta ji ta bakin wasu daga cikin abokan sana’arsa ta fim kuma uba a gare su, inda suka bayyana alhiinin rashin da suka yi, tare da mika sakon ta’aziyyarsu ga sauran ‘yan uwa da kuma iyalansa, ga dai bayanan na su kamar haka:
Alhassan Aliyu Kwalli (Shugaban kungiyar Kannywood):
Innalillahi wa inna ilaihur raji’un. Innalillahi wa inna ilaihirraji’un. Sunana Alhassan Aliyu kwalli shugaban kungiyar Jarumai na masana’anyar Kannywood.
Hakika wannan rashi na Alhaji Umar Yahaya wanda aka fi sani da Bankaura, rashi ne wanda mun sake samun wani gibi a wannan masana’anta wanda cike shi sai dai abin da Allah ya yi. Babu shakka mun kadu matuka da gaske da yadda ya kwanta jinya na rashin kafiya har kuma Allah ya kaddara ta wannan hanya Allah zai karbi rayuwarshi, babu shakka mun yi bakin ciki, mun yi alhini na rabuwa da wannan bawan na Allah, mutumin kirki, mutumin arziki, dattijo, kuma mutum ne wanda mu a tsawon zamanmu da shi ba mu san abokin rigimarsa ba.
Babu shakka kullu Nafsin za’ikatul Maut, duk musulmi jiran wannan rasuwa yake sai dai fatan Allah ubangiji ya sada shi da ma’aiki (S.A.W), Allah ya karbi shahadarsa, muma kuma in tamu ta zo Allah ya sa mu cika da kyau da imani. Bankaura kusan lokaci daya muka fara wannan harka sa shi, shi kansa wannan suna a zan manta ba a lokacin da zamu fara yin diramar NA DAKAMA a gidan talabijin na CTb, wanda yake da suna ARTb a halin yanzu, wannan dirama ta dan Kurma wato NA DAKAMA wato babban uba shi ma a cikinmu Malam Garba Ilu.
Hakika lokacin da za mu yi wannan da yake ana sa ran shi ne zai kamar sifotin akto wato zai taimakawa shi dan kurma a cikin wannan shiri na NA DAKAMA, an tambaya wanne irin suna ya kamata a sa masa,.muna zaune shi da kansa ya ce toh ko a sa BANKAURA?, mu kai ta dariya kuma daga baya aka tafi aka gina karakta wato yanayin da me dabi’ar Bankaurar za ta dace da shi, kuma ya yi kokari ya yi, toh tun daga nan ya samo wannan suna, kusan a yau muna kimanin shekara talatin da takwas ko da Tara muna tare da wannan bawan Allah muna aiki, ba mu taba samun sabani da shi ba, kullum sai nasiha sai shawarwari da yadda za a samu ci gaba a wannan rayuwa da kuma wannan sana’a tamu ta fim.
Babbar shaidar da ni na fi yi masa shi ne Malam Umar yana daga cikin mutanen da kowanne irin aiki muke yi idan aka kira ho Sallah to ba maganar a sake dora masa Kamera nemansa ma za ka yi ka rasa, sai daga baya za a iya dora masa nasa ka gane ya je sallah, tun mutane basa ganewa har suka gane. Wannan dabi’a tasa ta kokarin yin Sallah musamman kuma cikin Jam’i wannan abu ya tsaya mun sosai a zuciyata kuma ina kyautata zaton ubangiji Allah zai dubi wannan biyayya da yayi wa wannan addini kuma Allah ya gafarta masa Allah ya sa ya huta, Allah ya sada
shi da Manzon Rahma Sallallawa alaihi wasallam.
Darakta Ibrahim Bala:
A dan takaitaccen tarihin Umar Bankaura tun kusan 1980 ya sami wannan sunan, tun da sunansa na gaskiya Umar Yahaya Malumfashi, to ya samu wannan suna tun daga gidan CTV. Kuma ya yi fina-finai da dama tsawon shekaru 30 ya ke film, kuma shahararre ne wajen shirin barkwanci da kuma sauran fina-finai da ake shiryawa, sannan abokansa dai su ne, dan hakin, da su Samanja, Su Saugiji, su Baba Tambaya. Sannan a kwana kwanan nan inda aka fi saninsa da Yakubu Ka fi Gwamna cikjn shirin kwana casa’in. Anan Hausawa ya rasu, bayan masallacin Murtala a wani asibiti, bayan tsahon jinya da ya sha.
Gaskiya ya kan samu yabo a wajen mutane, sabida gaskiya shi mutum ne me kaifi daya, baya san kuma raini, dan ya dauki harkar fim sana’a sosai.
Zara’u Sale Fantami (Haj. Adaman Kamaye):
Hakika yau muna cikin alhini da rashi na dan uwanmu, abokin sana’ar mu, wanmu, ubanmu wato Umar Bankaura, wanda aka fi sani da Bankaura wato Umar Manufashi.
Tun tsahon sanina da bawan Allan nan ni dai babu wani abu da ya taba hada ni da shi na sharri, abokin aikina ne mun sha fitowa a mata da miji, ko ya fito mun a wa, dan a yanzu zancen ma da nake yi wallahi ba dan ubangiji Allah ya kari kwanansa ba shi ne zai fito a mijina a shirin KUNNEN kASHI, wato wani fim da kuke taka rawa akansa na musa me sana’a da ake kiransa kunnen kashi, dan labarin ya karbu yayi nisa a mijina zai fito ana shirye-shiryen biki kenan Ubangiji Allah kuma ya yi ikonsa.
A sanina da Umar Manufashi ban taba ji an ce ga abokin fadansa ba, ko kuma ga shi ya ciwo bashin wani ko an samu matsala a tare da shi, ni dai a nawa sanin kenan, amma da yake shi sani kogi ne, ban san wani ba ko ya san akasin haka akansa, amma mu Alhamdulillah mun zauna lafiya da shi, kuma munai masa addu’a Ubangiji Allah yadda ya karbi rabsa cikin rasalama Allah ya ba shi sa’ar shiga kabarinsa, Allah ya sa Annabi ya yi masa masauki ubangiji yayi musu rahma dukkan musulmin da suka riga mu gidan gaskiya.
Sannan ina mika sakon ta’aziyyata ga musulman duniya baki daya na rashin dan uwanmu musulmi da muka yi, sannan ina mika ta’aziyya ga iyalansa ubangiji Allah ya ba mu juriyar rashinsa baki daya, Allah ya yi masa Rahma.
Zainab Hassan Basarakiya (Saudat):
Assalamu alaikum warahmatullahi ta’ala wa barakatuhu, sunana Zainab Hassan Basarakiya, Saudat a cikin shirin Izzar so. Muna rokon Ubangiji Allah ya ji kan Babanmu yayi masa rahma, ya gafarta masa, yasa mutuwa hutu ce a gare shi. A zahiri ni dai gaskiya mutumin kirki ne, mun yi mu’amulanta da shi fina-finai yana fitowa a matsayin mahaifinmu da sauransu, gaskiya mutumin kirki ne ni dai a zahiri ba zan iya cewa ga wani aibunsa ba, na fili da badini, duk da yake rayuwa dai sanin gaibu sai Allah, amma a zahiri abin da ka sani an ce shi mala’iku ke dauka, toh abin da na sani a tsakani na rayuwa na dan Adam gaskiya mutumin kirki ne, sai dai mu yi fatan Allah ya jaddada rahma a gare shi, ya sa mutuwa ta kasance hutu a rayuwar duk wani dan musulmi baki daya, ya sa ya shiga cikin kabarinsa a sa’a, ya sadu da mala’ikun rahma cikin aminci.
Jibrin Salihu (Laku-Laku):
Sunana Jibrin Salihu wanda aka fi Sani da Laku-Laku dan wasan Hausa kuma ‘Producer’ a masana’antar Kannywood. Hakika rasuwar Umar Yahaya Manufashi Bankaura babban rashi ne da ya girgiza masana’antar Kannywood, kuma an yi rashin dattijo mai magana daya, abin da na sani da Yahaya Umar Manunfashi, sanin darajar dan Adan tare da cika alkawari, duk lokacin da kuka yi alkawari da shi ba ya sabawa ban taba jin abokin fadansa ba, ga kula da Sallah akan lokaci.
Karshen ganina da shi ne mun gaisa muka yi magana fuskarsa a sake cikin wasa da dariya, Ina mika sakon ta’aziyyata ga iyalansa da ‘yan uwasa da abokan sana’armu ‘yan uwa ‘Yan kannywood. Allah ya ji kansa da rahma ya sa aljanna ce makomarsa ameen.
Abba El-Mustapha:
Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un. Allah ya yi wa Babanmu Alhaji Umaru Malumfashi wanda aka fi sani da “KA FI GWAMNA” rasuwa. Muna Addu’ar Allah Ya jikansa ya gafarta masa kurakuransa ya sa Aljanna ce makomarsa.
Idan tamu ta zo Allah ya sa mu cika da kyau da imani.