’Yan kasuwar Alaba Rago da ke ƙaramar hukumar Ojo a Jihar Legas, wadanda yawancinsu daga Arewa suke, sun nemi gwamnatin jihar ta biya su diyya saboda rusau da aka yi musu.
Sun ce an rushe musu shaguna da kayayyakinsu da suka kai na biliyonin naira, ba tare da sanarwa ba.
- An Yi Bikin Mu’ammalar Al’Adu Na SCO Na 2025 A Beijing
- ECOWAS Za Ta Kaddamar Da Rundunar Yaki Da Ta’addanci Mai Jami’ai 260,000
Wasu daga cikin ’yan kasuwar sun zargi cewa an haɗa baki da jami’an gwamnati wajen aiwatar da rusau ɗin duk da yarjejeniyar da suka ce suna da ita da gwamnati.
Wazirin Sarkin Alaba Rago, Alhaji Adamu Katagum, ya ce ba za su yarda a ƙwace musu dukiya da suka tara tun shekaru aru-aru ba.
Haka kuma wasu ’yan kasuwar sun bayyana cewa rusau ɗin ya sa ɓata-gari sun sace musu kaya, wasu kuma sun ji rauni.
Wasu daga cikin ’yan kasuwar sun yi kira ga gwamnati da ta sake duba matsayar ta, inda suka ce kasuwar ce tushen rayuwarsu da iyalansu, kuma rushe ta zai kara jefa su cikin talauci da rashin aikin yi.
Haka kuma, sun yi barazanar kai ƙarar gwamnati kotu idan aka ƙi biyan su diyya, domin a cewarsu, an tauye musu haƙƙin kasuwanci da kuma dukiyar da suka shafe shekaru suna tarawa.
Sai dai gwamnatin Legas ta ce irin waÉ—annan ayyuka na rusau na daga cikin shirinta na zamanantar da manyan kasuwanni, don su dace da tsarin birane na zamani da kuma kare muhalli.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp