‘Yan kasuwan canjin kudaden waje a Jihar Kano sun koka kan yadda jama’a suka raja’a a cikin sana’arsu ta canjin kudade.
Sun bayyana cewa kutse da shiga sanaa’ar canji kudin kasashin waje da wasu masu zuwa cin arziki kasuwar Wafa ke yi kamar wanzami, mai siyar da abinci, mai yankan farce, mai sai da fiyo wata dukka sun tsindima cikin wannan sana’a ta canji na kudadan kasashin waje a kasuwar Wafa da ke Kano.
- Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana 12 Ga Watan Yuni, Ranar Hutu
- Zuba Ruwan Dagwalon Nukiliya Cikin Teku Da Japan Ke Shirin Yi Zai Illata Duk Fadin Duniya
Sun ce wannan babbar matsala ce domin kuwa akwai lokacin da aka sami wani mai sai abinci a kasuwar ya karbi kudi dala 5000 zai canza wa wani ya gudu da kudin kamar dai yadda Hon. Akibu Sani Lawan, daya daga cikin ‘yan kasuwan ya yi korafi.
Ya nemi sabon shugaban kungiyar kasuwar Wafa karkashin shugabancin Alhaji Sani Salisu Dada ya dau matakin tsarkake wannan sana’ar a lokacin da yake hirar da manema labarai a Wafa.
Haka kuma shi ma, Alhaji Sani Salisu Dada sabon shugaban kungiyar kasuwar canjin kudi na Wafa ya ce kasuwar na cikin matsaloli na rashin kudin gudanarwa, domin akwai matsalar rashin kudin biyan ‘yan shara, masu gadi, wanda hakan ta sa dole a nemi taimakon tafi da kungiyar.
Ya ba da kyautar naira miliyan guda domin daukar ma’aikata a kasuwar a lokacin bikin rantsar da shugabannin kungiyar da aka yi a ranar Litinin da ta gaba ta.
Alhaji Abdu Muhammad Aja ya ce akwai alama an samu ingantaccen shugabanci a kungiyar kasuwar Wafa ganin yadda sabon shugaban ke neman shawarar dattawa da sauran al’umma.
Jam’in hulda da jama’a na kungiyar kasuwar Wafa, Alhaji Abdullahi Adamu Isa wanda a kafi sani da Abdullahi Iyo Wafa ya ce wadannan matsaloli manyan ne a kasuwar kuma gazawa ce, sannan za a tsarkake da tantance duk wani wanda zai yi wannan harka a wafa.