Kungiyar al’ummar kudancin Kaduna mazauna ketare – Amurka (SOKADUSA) ta yi tir da kisan da aka yi wa mutane kusan 33 a kauyen Runji da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.
Kungiyar ta ce kisan da ya afku a ranar Asabar din da ta gabata, 15 ga Afrilu, 2023, ya yi sanadin asarar rayuka 33 tare da jikkata wasu ‘yan yankin da ba su ji ba ba su gani ba a kauyen Runji, wannan na daya daga cikin jerin kashe-kashen da ake yi wa mutanen yankin tun daga shekarar 2015.
A wata sanarwa da shugaba da Sakataren kungiyar Alice Osunde da Stanley Ayashim suka fitar, sun ce harin da aka kai na ba gaira ba dalili ya faru ne bayan watanni 4 da kisan gillar da aka yi wa wasu mutane 38 a yankin da suka hada da Malagum, Kamuru–Ikulu da kuma Abun (Broni Prono) suma duk a Kudancin Kaduna a 18 ga Disamba, 2022.