Jam’iyyar PDP a jihar Kebbi ta samu sabbin ‘yan majalisa takwas daga jam’iyyar APC mai mulki a Jihar.
Sabbin ‘yan majalisar dai sun hada da ‘yan majalisar tarayya biyar da kuma ‘yan majalisar jiha uku.
An yi zargin cewa tsarin da jam’iyyar APC ta bi wajen gudanar da zabukan cikin gida a jihar ne ya sa ‘yan jam’iyyar suka fice daga jam’iyyar inda da yawa daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar suka yi zargin cewa an yi watsi da su.
Sanata mai wakiltar mazabar Kebbi ta tsakiya, Adamu Aliero da Sanatan Kebbi ta Arewa, Yahaya Abdullahi ciki har da dan majalisar wakilai da ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.
Kazalika mambobin mazabar Aliero/Jega/Gwandu da Dandi/Arewa a tarayya, Muhammad Jega da Abdullahi Zumbo, sun fice daga APC zuwa PDP.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp