Gwamnatin Nijeriya ta sanar da kwaso karin wasu ‘Yan Nijeriya 125 da suka makale a kasar Sudan a ranar Asabar sakamakon ci gaba da rikici a kasar ta Sudan.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na hukumar NiDCOM, Abdur-Rahman Balogun, ya fitar ranar Asabar.
- Fadan Sudan Ya Hana Kananan Yara Samun Ilimi —UNICEF
- Rikicin Sudan: Kashin Karshe Na ‘Yan Nijeriya Sun Iso Gida
A cikin wani sako, ya ce jirgin Tarco Airline: ST-TAL B737-300 ne ya dauko su yau Asabar 24 ga Yuni, 2023, da karfe 10:45 na safe agogon Nijeriya dauke da ‘Yan Nijeriya 125.
A cewar majiyar hukuma, ta ce kiyasin lokacin isowa a Port Sudan (PZU) zuwa Juba (JUB) shi ne awannu 2 da minti 50.
Jirgin zai tsaya na tsawon awa daya a Juba kafin ya ci gaba da tafiya zuwa Abuja.
Jirgin zai ɗauki dauki tsawon awanni 3 da minti 30 daga Juba zuwa Abuja, jimlar awa 7 da 30 kenan.
“Ana sa ran jirgin zai isa Abuja da misalin karfe 5:45 na yamma agogon Nijeriya,” in ji Balogun.
Gwamnatin kasar ta dawo da ‘Yan Nijeriya kusan 2000 da suka tsere daga rikicin kasar Sudan cikin watanni biyu da suka gabata.