Jimillar ‘yan Nijeriya 376 da su ka maƙale a ƙasar Sudan sun iso Abuja lafiya sakamakon aikin kwaso su da Gwamnatin Tarayya ke yi.
Mai ba da shawara ga Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Miss Nneka Anibeze, ita ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta ba manema labarai a ranar Alhamis.
Ta ƙara da cewa kashin farko na mutanen da aka kwaso, wato mutum 94, sun sauka ne a daren ranar Laraba a jirgin Rundunar Mayaƙan Sama na Nijeriya samfurin Hercules C-130, yayin da sauran mutum 282 su ka sauka a jirgin kamfanin Air Peace.
Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta tsaya a filin jirgin sama na Abuja domin tarbar waɗanda aka ceto daga Sudan ɗin.
A jawabin maraba da ta yi masu, ministar ta yi godiya ga Gwamnatin Tarayya saboda tattaunawar fahimtar juna da ta yi da gwamnatin Sudan wadda har ta kai ga samun karɓar ‘yan Nijeriya tare da kwaso su daga ƙasar da yaƙi ya ɓarke.
Ta ce: “Mun yi murna da ganin sun iso lafiya kuma babu wani rai da ya salwanta. Sun sha matuƙar wahala amma mun gode wa Allah da su ka iso gida lafiya.
“Mu na gode wa Gwamnatin Tarayya saboda nasarar da aka samu a aikin ceto ‘yan Nijeriyar da ke Sudan. Mu na addu’ar a samu zaman lafiya a Sudan da ma kowane ɓangare na ƙasar nan.
“Yaƙi ba abu ne mai kyau ba. Kun dai ga yadda mutanen da su ka tafi karatu su ka zama ‘yan gudun hijira ba zato ba tsammani. Wannan ba kawai bala’i ne na ƙasa da ƙasa ba, a’a, bala’i ne kuma da ya shafi jinƙan rayuwar bil’adama.
“Za mu ba ko wannen su kuɗi N100,000 domin su yi kuɗin mota zuwa wajen iyalan su. Haka kuma mun tanadar da masauki a otal ga waɗanda aka kwaso ɗin har sai sun haɗu da iyalan su, yayin da kuma waɗanda ke buƙatar a duba lafiyar su an yi masu hakan.“
Minista Sadiya kuma ta bayyana cewa kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya umarta, babu wani ɗan Nijeriya da ke son ya tsere daga halin da ake ciki a Sudan da za a bar shi a baya.
Ta ce, “Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa da kuma Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje da sauran ma’aikatun gwamnati irin su NEMA, NCFRMI, NIDCOM, NIA da Rundunar Mayaƙan Sama na Nijeriya su na aiki tare da Ofisoshin Jakadancin Nijeriya da ke Sudan, Masar, Etofiya da Chadi domin tabbatar da cewa ko mutum ɗaya ba a baro ba. Don haka, dukkan ɗan Nijeriyar da ke so ya tsere daga halin da ake ciki a Sudan za a dawo da shi gida cikin tsaro da darajtawa.
“Aikin kwashe mutanen ya gudana ne ta hanyoyi masu wuyar sha’ani na wasu mutane da su ka zama dillalai a lamarin, wanda hakan ne ya sa aka riƙa fuskantar matsalolin da aikin ya ci karo da su. An shirya ci gaba da kwaso mutanen mu kuma aikin zai gudana da sauri-sauri fiye da da har sai an kwashe dukkan ‘yan Nijeriya da ke Sudan an kawo su gida.”
Ita dai Sudan, ta auka cikin rikicin yaƙi ne a ranar 15 ga Afrilu lokacin da wasu sassa na sojojin ƙasar masu adawa da juna su ka fara kai wa juna hari a birnin Khartoum da yankin Darfur.