ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A Nijeriya Ake Sarrafa Taliyar Indomie, Ana iya Amfani Da Ita Ba Matsala – Shugabar NAFDAC

by yahuzajere
3 years ago
indomie

An tunasar da ‘yan Nijeriya masu amfani da Taliyar Indomie da su sani cewa ana sarrafa ta ce a kasar nan ba wai ana shigo da ita daga kasar waje ba, haka kuma sinadaran da ake yin amfani da su wajen sarrafa ta na ethylene oxide ba a Nijeriya ake samar da shi ba.

Duk da cewa, Taliyar ta Instant Noodles, na daga cikin haramttauun kayan da aka haramta shigo da su cikin kasar nan, an shawarci masu yin amfani da wacce ake sarrafawa a Nijeriya da su saye ta su kuma yi amfani da ita.
Akwai fargaba ga wasu ‘yan Nijeriya ganin cewa ana magana a kan Taliyar ta instant Noodles a faɗin duniya a halin yanzu.

  • Shugabannin Da Aka Zaba Na Da Jan Aikin Hada Kan Nijeriya – Lawan

Da an yi maganar Taliyar ta noodles kawai ana ɗaukar Taliyar Indomie ake nufi.

ADVERTISEMENT

Wannan na faruwa ne ganin cewa Indomie na a kan gaba a  kasuwar da ta yi a fadin duniya a fannin sarrafa noodles.

Hakazalika, wannan matsayin ya zo ne daidai lokacin da ake son inganta Taliyar da rabar da ita.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

A 2022, wani rahoto da aka fitar a kasuwar da ke a Gabashi da Kudancin Afirka da aka wallafa a kafar yanar Gizo wato (COMESA) an gargaɗi ‘yan Kasar Masar kan su guji cin  wasu nau’uka na Taliyar Indomie Instant Noodles saboda zargin tana dauke da wasu nasadarai da za su iya shafar kiwon lafiyarsu.

Kamar a yankin Larabawa, fargaba ta ci gaba da yaduwa a kasashen da ke makwabta da iyakokin Masar.

Hakazalika, a Nijeriya wasu kafafen yaɗa labara sun ci gaba da wallafa rahoton da ya fito daga Masa. Inda suka ci gaba da jefa tsoro a zukatan ‘yan Nijeriya, inda hakan ya sa Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa NAFDAC da Hukumar kula da ingancin sarrafa kaya ta ƙasa (SON) suka shigo cikin lamarin tare da tsunduma kan yin aiki game da maganar guraɓatacciyar Taliyar da ake shigowa da ita cikin ƙasar nan ta hanyar fasa-ƙwaurin ta.

A ƙarshen bincike, an gano cewa, ba a saɓa ka’idar iyaka ba wajen shigo da ita kuma kasuwanninmu ba su fuskantar wata barazana.

An gano sanadarin na ethylene oxide a cikin Indomie na janyo cutar daji, a kasashen Taiwan, Malaysiya, inda bayanin da jami’an kiwon lafiyar kasashen suka yi ya haifar da raɗe-raɗi da jefa tsoro a cikin zukatan ‘yan Nijeriya.

Kafafen yada labara sun ci gaba da ƙara gishiri a miya tare da yin kanun labarai masu zafi don jefa fargaba a zukatan jama’a.

Kamfanin sarrafa taliyar ta Indomie a Taiwan da Malaysia da kuma kamfanin Dufil Prima Food Plc  da ke a Nijeriya  da ke sarrafa Indomie Instant Noodles a cikin kasar nan su ma an tantance su don guje wa kalubalen na cikin gida.

A hirarta da manema labarai, Darakta Janar ta NAFDAC, Mojisola Adeyeye ta sanar da cewa, Taliyar ta Instant noodles, na daga cikin kayan da gwamnatin tarayya ta haramta shigowa da su cikin kasar nan, inda ta ce, ita Taliyar da ake magana a kai hukumar ba ta yi mata rijista ba kuma sannan ba a Nijeriya ake sarrafa ta ba.

Ta ce muna yin takatsantsan don ganin ba a yi fasa-kwauarin ta zuwa cikin Nijeriya ba.

Shugaba sashen sadarwa da shirya tarurruka na kamfanin Dufil Prima Foods Plc, Tope Ashiwaju, ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa, ɗaukacin  nau’o’in Taliayarta Indomie Instant Noodles a cikin kasar nan ake sarrafa su kuma bisa doka da oda.

“Muna bin ƙa’idar inganci sau da ƙafa da Hukumar NAFDAC da Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki ta Ƙasa (SON) suka shimfiɗa a dukkan kamfanonin sarrafa kayanmu. Muna amfani ne kawai da kaya masu inganci da ake samarwa daga sahihan masu kawo kaya kuma ana duba na’urorin da muke aiki da su a kai a kai tare da tantance su domin tabbatar da cewa suna da ingancin da ya kamata.” In ji shi.

indomie
yahuzajere
+ postsBio
  • yahuzajere
    Da Kujerar Mulki Gara Zaman Lafiyar Kano
  • yahuzajere
    Ya Kamata Amurka Ta San Ana Barin Halal Don Kunya
  • yahuzajere
    Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Ga Gwamnatin Tarayya A Kan Tozarta Marasa Lafiya Daga Jami’an FIRS A Kano
  • yahuzajere
    Sin Ta Kaddamar Da Gagarumin Bikin Ba Da Lambobin Yabo Na Kasar Sin

MASU ALAKA

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi
Labarai

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”
Ra'ayi Riga

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma
Labarai

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Next Post
An Sanya Sunan Pele Cikin Kamus A Brazil

An Sanya Sunan Pele Cikin Kamus A Brazil

LABARAI MASU NASABA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.