‘Yan Nijeriya sun nuna damuwarsu kan yadda Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya maida hankali wajen sanya hannu kan dokar canza taken Nijeriya zuwa ga koma wa amfani da tsohon na da baya maimakon duba wahalhalun da suke sha.
A ranar Laraba ne dai, Shugaban Tinubu ya tattaba hannu kan dokar komawa amfani da tsohon taken Nijeriya, lamarin ya biyo bayan gabatar da kudurin da amincewa da shi da ‘yan majalisun wakilai da na dattawa suka yi ne a makon jiya.
- Majalisar Wakilai Za Ta Binciki CBN Kan Korar Ma’aikata 600
- Sojojin Nijar Sun Cafke Kasurgumin Dan Bindigar Da Ya Addabi Zamfara
Sai dai kuma kafin sanya hannu kan dokar, Babban Antoni kuma ministan shari’a (AGF) Lateef Fagbemi, SAN, ya bukaci ‘yan majalisun dokokin kasa da ka da su amince da kudurin doka da ke neman a koma amfani da tsohon taken Nijeriya a maimakon wanda ake amfani da shi a halin yanzu.
Fabgemi ya kuma yi gargadin cewa ka da ‘yan majalisun su yi riga malam masallaci wajen canza taken kasar nan, amma duk da wannan kiran nasa ‘yan majalisu sun ci gaba da aikinsu har ta kai ga shugaban kasa ya sanya hannu, inda yanzu kudurin ya zama doka.
Ministan wanda ya nuna adawarsa kan sauya taken a wajen taron jin ba’asi kan kudurin wanda kwamitin majalisar dattawa kan shari’a, kare hakkin Bil’adama da harkokin shari’a ta shirya a ranar Litinin a Abuja, Fabgemi ya yi gargadin cewa ka da ‘yan majalisa su yi amfani da karfin majalisa wajen amincewa da kudurin ba tare da bai wa ‘yan kasa damar tofa albarkacin bakinsu ba.
Ya lura bisa kan cewa bai kamata a je ga kokarin gyara dokar da za ta kai ga canza taken kasa zuwa tsohon na da a kan wanda ake tafiya a tare da shi a halin yanzu ba tare da shigo da kowa da kowa cikin lamarin ba.
“A wasu lokutan taken kasa na fito ne daga irin gasa daga wajen ‘yan kasa. Misali za a iya baje taken kasar da ake da shawara a kai a tafka muhawa kafin a kai ga amincewa ko ayyanawa.
“Babban abun nufi a nan shi ne, a samar da taken da ke da ra’ayin jama’a da goyon bayansu domin tabbatar da cewa taken ta tafi daidai da muradinsu, zamantakewa da kuma siyasar wannan zamanin.
“Don haka ina adawa da ra’ayin kawai a ce tunanin canza taken kasa zai fito ne daga wajen ‘yan majalisa ko shugaban kasa kawai.
“Maimakon hakan a ji yo ra’ayoyin jama’an kasa kan tunanin canza taken kasa, walau a koma amfani da na da baya ko kuma a kirkiro sabo, don haka akwai bukatar a gudanar da jin ba’asin jama’a a shiyyoyi tare da tattaro shawarwarin shugabannin tarayya, jihohi, ‘yan majalisun tarayya da na Jihohi, da sauransu.
“Ta hakan ne za a samu nasarar fito da hakikanin abun da masu rinjaye na kasar ke da bukata.”
Shi ma da yake gargadin ‘yan majalisun kasa, wani fitaccen lauya, Cif Mike Ozekhome (SAN), ya yi kira da a tattaro shawarori da ra’ayoyin ‘yan kasa daga lungu da sako kafin a yi maganar canza taken na kasa.
A cewarsa, ta hakan ne ra’ayoyin ‘yan kasa gabaki daya zai gamsu kuma za a samu nasarar fito da abun da za su yi na’am da shi.
Sai dai dan majalisar wakilai, Mohammed Shehu Fagge, ya yi suka ne kan matakin da aka dauka na dawo da tsohon taken, inda ya yi tsokaci cewa, kawo wannan magana na sauya taken rashin sanin ciwon kai ne.
Shehu, ya ce a wannan hali da ‘yan kasa ke ciki na yunwa, fatara da rashi da sauran abubuwa makamantansu su ya fi dacewa a mayar da hankali a kai.
Ya ce shugabanin majalisa ba su yi tunani ba, domin ba shi ne abin da ‘yan kasa ke so ba.
Ya ce kamata ya yi a kalli dokoki da za su amfana wa talakan kasa da abubuwa da za su kawo wa rayuwarsu sauyi.
Shehu ya ce har yanzu majalisa ba ta kammala aiki kan kasafin kudin 2024 ba, saboda haka yana kira da a fuskanci bukatun al’umma.
Shi ma wani dan Nijeriya mazaunin Jihar Bauchi, Ibrahim Muhammad, ya shan mamakin wannan matakin, “Ban san mene ne asalin dalilin da ke boye wajen canza taken kasar nan cikin kankanin lokaci ba, tun daga gabatar da kudirin zuwa amincewa da shi na fara tunani a kan kudirin. Gaskiya a halin da muke ciki na yunwa da fatara kar a dame mu da batun komawa tson taken kasa, a yi mana abun da ya dace ba.
“Ya kamata ko su ‘yan majalisu ba su yi zurfin tunani ba, ina dauka shugaban kasa zai yi abun da ya dace amma kash, gaskiya ba mu tsammaci hakan ba, dubban ‘yan kasa zai yi wuya su iya haddace wannan taken da aka koma, abun kunya ne ‘yan kasa su kasa iya karanto takensu, da yunwa za mu ji ko da wani haddace sabon taken da aka canza,” ya shaida.