Akalla ‘yan Nijeriya miliyan 31,800 ne ke fama da matsalar karancin abinci sakamakon tabarbarewar tsaro da cire tallafin man fetur wanda ya haifar da matsi da tsadar rayuwa.
Wannan adadi a cewar shirin abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP), ya zarta adadin mutanen da suka fada matsananciyar yunwa a irin wannan lokaci a bara da ya kai mutum miliyan 18,600.
- Haɗarin Kwale-kwale Ya Sake Ajalin Mutane 5 A Jigawa
- Haɗarin Kwale-kwale Ya Sake Ajalin Mutane 5 A Jigawa
Wasu bayanan hadin gwiwa da hukumomin kasa da kasa na abinci da lafiya da kuma na agaji suka fitar a ranar Laraba, sun ce halin matsananciyar yunwar da ake ciki a Nijeriya lamari ne mai ba da tsoro.
Rahoton ya ce matsalar tsaro ta hana manoma da dama iya gudanar da harkokinsu na noma, lamarin da ya haddasa karancin abinci, yayin da a bangaren guda hauhawar farashi ke hana mutane iya sayen kayan abincin da ake shigowa da su daga kasashen ketare.
Ƙungiyoyin sun ce matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na cire tallafin man fetur ya taka muhimmiyar rawa wajen haddasa matsalar karancin abinci da kuma tsadarsa ta yadda magidanta da dama ba sa iya ci su koshi.
WFP da kungiyar agaji ta Jamus GIZ da kuma Global Alliance da ke sanya idanu kan hada-hadar abinci mai gina jiki a kasashe, sun ce wannan matsala ta jefa rayuwar miliyoyin mata da kananan yara a hatsari cikin a Nijeriya.