Shugaba Buhari ya ce za a iya kawar da mafi yawan kalubalen da ke addabar al’ummar kasar nan idan har da gaske ‘yan Nijeriya suka yi amfani da koyarwar addininsu.
A sakonsa na sallah ga ‘yan Nijeriya, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ya kamata ‘yan Nijeriya su yi amfani da addini a matsayin abin da zai karfafa soyayyar bil Adama a tsakaninsu.
- NAHCON Ta Nemi Afuwa Kan Gaza Kwashe Maniyyata 1,551 Zuwa Aikin Hajji
- ‘Yan Nijeriya Sun Yi Alhinin Rasuwar Babban Sakataren OPEC Sanusi Barkindo
A cewar wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa Buhari ya fitar, ya ce da ‘yan Nijeriya za su yi amfani da koyarwar addininsu, da an magance mafi yawan abubuwan da suka addabi al’umma.
“Mutane suna yin addini ba tare da tsoron Allah ba; suna sa rayuwa ta yi wa wasu wahala; kudi ya zama Allahnsu; Shugabanni sun watsi da rantsuwar da suka yi ta hanyar karbar kudaden da ake bukata don jin dadin jama’a suna karkatar da su zuwa aljihunsu a boye.
“Cutar da jama’a da ‘yan kasuwa ke yi da sace-sacen jama’a da ma’aikatan gwamnati da sauran masu rike da amanar jama’a ke yi, ya nuna yadda aka yi watsi da koyarwar addininmu.
“Bai kamata a yi amfani da addini kawai a matsayin alama ta ainihi ba, sai dai a matsayin kyautata ruhi don kyautatawa kasarmu da bil Adama.”
Yayin da yake taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar Idi, Shugaba Buhari ya shawarci Musulmi da su “Kyautata kyawawan dabi’un Musulunci ta hanyar misalai da kuma aiki da su,” ya kara da cewa, “Musulmi su guji cudanya da muggan ra’ayoyin masu tsattsauran ra’ayi da suka yi wa Musulunci mummunar fahimta.”
Dangane da kalubalen tsaro da tsadar rayuwa a kasar, shugaba Buhari ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa “ba zan huta ba har sai na kawo wa ‘yan Nijeriya sauki,” ya kara da cewa “na san matsalolin da mutane ke fuskanta kuma ina kokarin magance su. .”
Ya kuma ba da bayani na musamman ga jami’an tsaro da ke yaki da ta’addanci ta bangarori da dama da iyalansu, da kuma garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su.