Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce wahalar rayuwa a ƙarkashin Shugaba Bola Tinubu ta yi tsanani matuƙa, har wasu ‘yan Nijeriya sun fara kewar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Amaechi ya bayyana haka a Abuja, ya ce, “Tashin farashi ya kai ƙololuwa. Mutane ba sa iya siyan abinci. Komai ya lalace.”
Amaechi, wanda ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC, ya ce bai taɓa ganin Tinubu a matsayin wanda ya dace da shugabanci ba.
Amaechi ya soki faɗuwar darajar naira. Ya ce, “Dalar Amurka tana kusan ₦460 a lokacin Buhari, yanzu kuma ta kai ₦1,580.” Ya ce sauya gwamnati kaɗai ba zai wadatar ba, ya kuma buƙaci a samar da sabuwar tafiyar da jama’a za su jagoranta.
Haka zalika, tsohon Antoni Janar, Abubakar Malami, shi ma ya fice daga APC. Dukansu sun koma jam’iyyar adawa ta ‘African Democratic Congress’ (ADC), yayin da jam’iyyar ke shirin tsayawa takara a zaben 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp