A halin yanzu ‘yan Nijeriya, ba tare da banbancin siyasa, addini ko bangaranci ba suna nuna mamakinsu a kan yadda kasar nan ta samu kanta a wannan hali na tabarbarewar tattalin arziki da tsadar rayuwa. Rayuwa ta yi arha amma abin da rayuwar za ta ci ya yi matukar tashi kamar na gwauron zabo, wannan kuma ya sabawa dukkan ka’idoji na dimokuradiyya wadanda ta yi wa al’umma alkawarin ingantaciyar rayuwa.
Wannan ba kuma yana nufin cewa, Nijeriya ta taba tsallakawa tudun muntsira ba ne, amma abin da ke tayar da hankali shi ne yadda aka yi wa al’umma alkawari tare da shafa masu romon baka amma kuma sai gashi rayuwa ta zama abin da ta zama, al’umma na fama da yunwa a sassan kasa, ‘yan siyasa sun kasa cika alkawuran da suka yi a lokacin da suke yakin neman zabe.
- Shugaba Tinubu Ya Gana Da Gwamnoni Kan Ƙalubalen Da Nijeriya Ke Fuskanta
- Nijeriya Za Ta Shawo Kan Ƙalubalen Da Take Fuskanta Nan Gaba Kaɗan – Ganduje
Abubuwan da suka faru a jihohin Neja da Kano da wasu wuraren a sassan Nijeriya alamu ne da su ke nuna cewa, nan gaba kadan ‘yan Nijeriya za su fito su nemai a yi masu adalci saboda daga dukkan alamu ‘yan Nijeriya sun fusata. A yayin da al’umma suka yi kumajin fitowa don nunan rashin amincewarsu da matsalolin da ake fama da su na yunwa da tsadar rayuwa wadanda suke ya kama hanyar durkusar da dukkan sassan tattalin arzikin kasa, to lallai alama ce da ya kamata shugabanni su dauka da muhimmanci.
A Kano, masu zanga-zangar ba suna neman a basu wani abu daban ba ne, suna neman a sama masu abubuwan da zai kawo musu saukin rayuwa ne kamar abinci, saukin kudin makaranta da kuma uwa uba a kawo masu saukin matsalar tsaro da ta addabi al’umma ta yadda za su iya barci ba tare da wata fargaba ba. Sun kuma nemi a bude iyakokin kasa ta yadda za a samu shigo da abinci da sauran kayayyaki don taimaka wajen kawo saikin wadanda ake samar wa a cikin gida.
Idan za a iya tunawa an kulle iyakokin kasar nan ne domin dakile yadda ake shigo da kayan abinci saboda yadda manoma suka yi korafin cewa, shigo da kayan abinci yana durkushe kokarin da suke yi na samar da abinci a cikin gida, amma shin wannan mataki na kulle iyakoki za mu iya cewa, kwalliya ta biya kudin sabulu kuwa?
Matsalolin da rufe iyakokin kasar nan ya haifar yana ci gaba da illata al’umma da kuma mummunar shawarar da aka ba gwamnati ta kara kudaden haraji a akan wasu kayan gona da ake shigowa dasu daga kasashen waje. Gwamnati ta sa burin tattaro kudaden haraji koda kuwa mutane za su rasa rayukansu ne. tabbas wadannan manufofin na gwamnati basu da alfanu ga rayuwar al’umma.
A ra’ayinmu, kamar mutum da aka kai shi bango, alamu yana nuna mutane na yi wa manufofin gwamnati tutsu kamar yadda muka gani a wasu sassan Nijeriya a ‘yan kwanakin nan. Ko ‘yan NIjeiya na nuna cewa, takurawar ya isa haka nan ne? wannan kuma yana nuna cewa, duk wanda aka takura ba wanda ya isa ya san abin da zai iya yi na tawaye a nan gaba.
Matsalolin da kulle iyakokin kasar ta haifar da karin haraji a kan kayan abinci da ake shigowa da sun kara tabarbarewar matsalar staro, abin da ya sa manoma basa iya zuwa gonakinsu haka ma in lokacin girbi ya yi sai sun samu izinin ‘yan ta’adda da kuma yadda aka muhimmantar da dala a sha’anin tattalin arzikin kasar nan duk sun jefa al’umma cikin matsaloli da tsadar rayuwa.
Ga dukkan wadanna matsalolin martanin gamnati mai ci bai wadatar ba, sai wai gashi ana cewa, ‘yan Nijeriya cewa, abinci ya fi arhra fiye da koina a Afirka, tabbas wanna karya ne tsagwaronta, muna bukatar sanin wanda ya yi wannan bincike da kuma wace hujjoji ya yi amfani da ita.
Bayan haka kuma sai ga shi kuma ana neman mayar da matsalar ta zama tamkar siyasa, ana neman a ce, ‘yan Nijeriya sun zama wawayen da har sai da ‘yan adawa ne ke amfanai da su wajen bayyana halin da suke ci na matsin rayuwa, wannan abin takaici ne.
Gaskiya a halin yanzu al’umma na cikin yunwa, ‘yan Njjeriya na fuskantar yunwa da suna kuma cikin haushi kuma akwai rudewa na sanin ainihin anihin abin da ya kamata su yi. Amma kuma rikicin shi ne in har aka samu rudewa da yunwa da kuma fushi abubuwa sun lalace, ya kamata gwamnati a dukkan mataki su dauki matakin yayyafawa al’amarin ruwa don kada al’marin ya zama wani abu daban.
Ya kamata kada ‘yan siyasa su raina al’umma, musamman ganin sune suka kai matakin da suke a halin yanzu, ba wai a ce wa talakawa su yi ta hakuri ba tare da jiran tsammani, in har haka gaskiya ne me ya sa su masu tafiyar da mulki wani irin hakuri suke yi a wajen tafiyar da rayuwar su.?
A ra’ayinmu, ya kamata gwamnati ta fuskanci nauyin da al’umma suka dora musu su kuma fahimci cewa tabbas ana fuskantar yunwa a sassan kasa, mutane na mutuwa saboda rashin abinci. Al’umma na kukan yunwa!!