‘Yan Nijeriya daga sassa daban-daban sun bayyana alhininsu bisa rasuwar Sakataren Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Mai ta Duniya (OPEC), Dakta Muhammadu Sanusi Barkindo.
Tuni dai aka yi jana’izar marigayin a mahaifarsa ta Yola da ke Jihar Adamawa.
Babban limamin masallacin Juma’ar Mai Martaba Lamido Adamawa, Dakta Muhammadu Barkindo Aliyu Mustafa, Grand Khadi Ibrahim Bobbo, ya jagoranci gudanar da jana’izar.
Dakata Muhammadu Sanusi Barkindo ya rasu yana da shekaru 62 a duniya, yana mata biyu da da guda daya.
Manya-mayan mutane da shugabanni daga sassa da dama a ciki da wajan kasar nan ne suka halarci sallar jana’idar.
Har kawo lokacin hada wannan rahoton iyalan mamacin ba su kai ga bayyana dalilin rasuwarsa ba.
Sai da a ranar Talata da ta gabata, Marigayi Sanusi Barkindo, da tawagar kungiyar OPEC sun ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari, inda shugaban ya yaba masa da cewa ya zame wa Nijeriya wakili na kwarai a mukamin sakataren kungiyar na shekaru shida.
Labarin rasuwarsa ta zo wa jama’ar Jihar Adamawa bagatatan, inda ta jefa jama’a cikin jimami da alhini na wannan rashin babban mutum.