‘Yan Nijeriya sun yi fatali da shirin hukumar kula da harkokin wutar lantarki (NERC) na rage kudin wutar lantarki da suke yi a ajin A wato ‘yan ‘Band A’ daga kan naira 225 zuwa naira 206.8 kan wutan da suka sha na sa’a guda.
Kungiyar Kwadago na NLC da TUC da kungiyar kwastomomin da ke amfani da wutar lantarki da kungiyoyin farafen hula sun shaida wa jaridar Punch bukatarsu na a gaggauwa ta sake nazari kan karin kudin wutar lantarki.
- Almundahana: Kotu Ta Bayar Da Belin Hadi Sirika Da ‘Yarsa
- Tsaron Yanar Gizo: TUC Ta Yi Barazanar Shiga Zanga-zanga A Nijeriya
Sanarwar sabon farin wutar da NERC ta yi na zuwa ne kwanaki 33 bayan da ta tsula karin farashin ga ‘yan rukunin ‘A’ daga kan naira 68 na kudin wuta da suke sha a sa’a guda zuwa naira 225, lamarin da ke nuni da cewa an kara kudin wuta da kaso 240.
Kan karin kudin, gwamnatin tarayya ta ce hakan zai ba ta damar samun rarar naira tiriliyan 1.5.
Bugu da kari, majalisar wakilai, kungiyoyin kwadago da na lauyoyi sun yi tir da karin kudin wutar lantarki da ya shafi sama da kwastomomi miliyan 1.9.
Majalisar wakilai ta yi kira ga NERC da ta janye shirinta na karin kudin wutar lantarki a fadin kasa, yayin da kungiyar kwadago ta bayar da wa’adin mako biyu da a sake nazarin karin kudin wutar lantarki cikin gaggawa.
Sai dai, ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya dage kan dole fa ‘yan kasa su amince da karin kudin, yana mai cewa idan zuwa nan da wata uku ba a aiwatar da karin farashin ba, to kuwa al’umman Nijeriya za su rasa wutan ma baki daya.
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan lamarin, mataimakin shugaban kungiyar TUC, Tommy Etim, ya ce, “Ba zai yuwu a amince da hakan ba. Gaba daya muna son a janye batun karin kudin wutar nan.”
Shi ma ma’ajin kungiyar NLC, Hakeem Ambali, cewa ya yi, “Wannan lamarin ya kasance abun damuwa matuka ga kungiyar kwadago, muddin ba wai samun karuwar wuta aka yi ba, kowani irin karin kudin da aka yi na wuta ba abun lamunta ba ne.”
Shugaban kungiyar NACCIMA, Dele Oye ya ce kamfanonin rarraba wutar lantarki a Nijeriya ba su da dalilin da za su buga karji su yi karin kudin wutan lantarki. Ya ce akwai bukatar masu ruwa da tsaki su sa baki wajen ganin an janye batun baki daya.
Shugaban NACCIMA ya ce muddin ba a samu ra’ayin masu ruwa da suka hada da kamfanoni, ‘yan kasuwa, masu amfani da wuta da kungiyoyin fararen huda ba wajen tattauna yadda za a yi karin kudin.