‘Yan kwallon Real Madrid ne suka mamaye ‘yan wasan Champions League 11 da za su iya fuskantar zakarun kowacce nahiyar duniya a kakar 2021/22.
BBC ta rawaito cewa, duk bayan kammala kakar Champions League, hukumar kwallon kafar Turai kan fitar da 11 da ba kamarsu a gurbin da suka taka leda a gasar a kakar.
Ranar Asabar Real Madrid ta yi nasara a kan Liverpool da ci 1-0 a birnin Paris din Faransa ta lashe Champions League na kakar nan, sannan na 14 jumulla.
Golan Real Madrid, Thibaut Courtois shi ne ya karbi kyautar dan wasan da yafi taka rawar gani ranar Asabar, bayan da ya hana kwallaye da yawa shiga ragarsa.
Bayan karkare kakar bana, Karim Benzema ne ya lashe kyautar gwarzon Champions League, wanda ya zura kwallo 15 a wasannin 12 a bana.
Shi kuwa Vinicius Jr. wanda ya ci Liverpool kwallon, an bayyana shi a matakin matashin da ba kamarsa a babbar gasar Zakarun Turai ta kakar nan.
Mai sekara 21 ya ci kwallo hudu ya kuma bayar da shida aka zura a raga a kakar ta 2021/22.
‘Yan Real Madrid hudun daga fitattu 11 a Champions League sun hada da Benzema da Courtois da Modrić da kuma Vini Jr.
Sauran sun hada Alexander-Arnold da Van Dijk da Robertson da kuma Fabinho dukkansu daga Liverpool da dan kwallon Chelsea, Rüdiger da De Bruyne na Manchester Cit da dan wasan Paris St Germain Kylian Mbappé.