Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna tayi nasarar cafke daya daga cikin fursunonin da suka arce daga gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja.
Kakakin Rundunar, DSP Muhammad Jalige ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar jihar a ranar Litinin a Jihar.
Jalige ya ce, fursunan mai suna Ali Shuaibu, jami’an rundunar sun kama shi ne a jiya Lahadi, inda ya kara da cewa, fursunan mai shekaru 60 dan asalin jihar Kano ne.
Kakakin ya ci gaba da cewa, an cafke Ali ne a wani yanki a Kaduna, a yayin da yake kokarin shiga jihar Kano, inda ya kara da da cewa, bayan rundunar ta bincike shi ya amsa cewa, yana daya daga cikin fursunonin da suka gudu daga gidan gyaran halin na Kuje.
Ya bayyana cewa, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, Yekini Adio Ayoku ya bayar da umarnin cewa, Jami’an su mika Ali ga mahukuntan gidan gyara halin na Kuje.
Jalige ya ce kwamishinan ya jinjina wa jami’an rundunar kan kokarinsu, inda ya kuma bukace su dasu kara yin kaimi wajen yaki da ta’addanci da yan ta’adda a fadin jihar.