Rundunar ‘yan sandan Jihar Ondo ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen kashe wani direban mota har lahira a Jihar.
Fusatattun jama’a a yankin sun kuma cinnawa motar direban wuta.
- Kotu Ta Sake Turawa Rarara Sammaci Kan Taurin Biyan Bashi A Kano
- Majalisar Dokokin Jihar Filato Za Ta Ci Gaba Da Zama A Garkame – Kwamishinan ‘Yansanda
Wasu ’yan daba ne suka kashe marigayin a unguwar Ijoka da ke cikin birnin saboda tukin ganganci.
Mutane biyu ne suka mutu a lamarin a ranar Litinin yayin da wasu shida suka samu raunuka.
Sai dai sa’o’i bayan faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Ondo, SP Funmilayo Odunlami, ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an gudanar da bincike kan lamarin.
Ta yi nuni da cewa har yanzu ba a tabbatar da cewa marigayin dan damfara ne a yanar gizo ba kamar yadda wadanda suka kashe suka zarge shi.
Hakan na faruwa ne yayin da ya yi kira ga jama’a da su rika kai rahoton irin wannan lamari ga jami’an tsaro kuma kada su dauki doka a hannunsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp